Sojoji sun yi wa yan ta'addan Boko Haram kwantan bauna, sun tura su lahira

Sojoji sun yi wa yan ta'addan Boko Haram kwantan bauna, sun tura su lahira

  • A cigaban da kokarin dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin Najeriya, Sojin Operation Haɗin Kai sun ƙara samun nasara kan Boko Haram
  • Sojoji tare da haɗin guiwar jami'an CJTF sun yi wa wata tawagar mayaƙan Boko Haram kwantan ɓauna, sun halaka uku
  • Bayanai sun nuna cewa Sojojin sun yi nasarar kwato bindigun AK-47 da wasu makamai da kayan aikin yan ta'addan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Dakarun rundunar Operation Haɗin Kai da ke aiki a arewa maso gabashin Najeriya sun yi nasarar halaka mayaƙan Boko Haram uku a wani kwantan ɓauna da suka musu a safiyar Talata.

Leadership ta rahoto cewa Dakarun sojin sun kai wa yan ta'addan samamen ba zatan ne da taimakon jami'an tsaron Civilian Joint Task Force (CJTF).

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Sojoji sun kakkabe mafakar IPOB/ESN, sun kwato makamai masu hadari

Abubuwan da sojoji suka kwato.
Sojojin sun yi wa yan ta'addan Boko Haram kwantan bauna, sun tura su lahira Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Dakarun tsaron sun yi wa yan ta'addan kwantan ɓauna, kana suka farmake su a kan hanyar ƙaramar hukumar Gubio, da ke jihar ta Borno.

Masani kuma mai sharihi kan al'umar tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya tabbatar da nasarar dakarun sojin ga wakilin jaridar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda lamarin ya faru

Ya ce sun samu nasarar kwantan baunan ne kan wasu mayaƙan kungiyar Boko Haram da suka farmaki makiyaya kuma suka tattara musu dabbobi suka nufi hanyar da zata haɗa su da Dutsen Mandara, da ke yankin Gwoza.

Majiyar ta ce:

"Dakarun rundunar sojojin Najeriyan sun yi nasarar aika mayaƙan Boko Haram guda uku lahira kuma suka kwato bindigun AK-47 guda biyu."
"Sojojin sun kwato kwari da baka da bindigar AK-47 mai carbi, Babur guda ɗaya da sauran kayakkaki daga hannun yan ta'addan, waɗan da suke amfani da su wajen kai hari."

Kara karanta wannan

Rikicin APC a mazaɓar Ahmad Lawan ya bude sabon shafi, wani ɗan takara ya maka Machina a Kotu

A wani labarin kuma Ambaliya da iska mai tsanani sun lakume rayukan mutane, gidaje sama da 2,000 sun halaka a Kano

Wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya halaka mutum uku da wasu gidaje sama da 2,000 a kananan hukumomi 5 a jihar Kano.

Shugaban hukumar SEMA, Dakta Sale Jili, ya ce tuni hukumar ta kai ɗaukin gaggawa yankunan da abun ya shafa tare da tallafa wa mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262