Sun Harbe Ni Sau 2 Amma Harsashin Bata Ratsa Ni Ba, Fasto Da Ya Biya N1m Ya Fansa Kansa Daga Yan Bindiga

Sun Harbe Ni Sau 2 Amma Harsashin Bata Ratsa Ni Ba, Fasto Da Ya Biya N1m Ya Fansa Kansa Daga Yan Bindiga

  • Wani fasto a Jihar Rivers mai suna Apostle E. S. Samuel na cocin Divine Promise Christian Church of God ya magantu kan yadda masu garkuwa suka sace shi
  • Apostle Samuel ya ce ana ruwan sama suka taho cocinsa suka kama shi, suka harbe shi sau biyu a cinya amma harsashi bai ratsa shi ba don haka suka caka masa wuka
  • Amma daga bisani faston ya ce sai da mutanensa suka biya kudin fansa har Naira miliyan ga masu garkuwar kafin suka sako shi ya koma gida

Rivers - Shugaban cocin Divine Promise Christian Church of God, Apostle E. S. Samuel, ya bada labarin yadda masu garkuwa suka sace shi daga cocinsa a Umulu Etche a Jihar Rivers suka daba masa wuka a cinya bayan sun harbe shi sau biyu da bindiga amma harsashin ba su ratsa jikinsa ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Matar Ciyaman Din NULGE Na Jihar Zamfara Da Cikin Wata 9

Masu garkuwan sun kutsa cocin da ba a dade da ginawa ba a Umulu Etche, Jihar Rivers misalin karfe 6.35 na dare a ranar 17 ga watan Yuni suka sace faston.

Taswirar Jihar Rivers.
Sun Harbe Ni Sau 2 Amma Harsashin Bata Ratsa Ni Ba, Fasto Da Ya Biya N1m Ya Fansa Kansa Daga Yan Bindiga. Hoto: @daily_trust.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke bada labarin abin da ya faru da shi hannun wadanda suka sace shi, Apostle Samuel ya fada wa SaharaReporters cewa masu garkuwan sun kai shi wurare daban-daban a daji kafin suka tsaya a wuri daya, suka harbe shi sau biyu a kafa amma harsashin bai shiga ba, sun caka masa wuka sannan suka masa duka.

Sun harbe ni bindigar bata ratsa ni ba amma sai da na biya N1m kudin fansa, Fasto

Ya ce:

"Ina cikin cocin lokacin da makiyayan suka shigo cocin suka sace ni. Ana ruwan sama suka min duka. Sun harbe ni sau biyu a kafa amma bai shiga ba, suka caka min wuka kuma suka tafi da ni daji suka nemi Naira miliyan 5.

Kara karanta wannan

Rashawa? Dalilai masu karfi guda 5 da suka sa shugaban alkalai ya ajiye aikinsa

"Na roke su cewa ba ni da kudi kuma suka tambaye ni; nawa zan iya nemo wa sai na fada musu N500,000 amma suka ce dole sai ya kai a kalla Naira miliyan 1.
"Kafin ka sani, mutane na sun tara kudin kuma su (masu garkuwar) suka musu kwatancen inda za su ajiye kudin kuma bayan kwana daya, suka karbi kudin sannan suka kira wanda ya ke tare da ni ya sake ni."

Faston ya cigaba da cewa yana da wayoyin salula biyu Iphone da kirar Samsung suka ce ya zabi daya, sai ya basu Iphone din.

"An bawa yan sanda lambar IMEI na Iphone din a Abuja. A cewarsu, suna jira lokacin da masu garkuwar ko kuma wanene suka siyarwa ya kunna, za su iya gano inda ya ke."

Dogo Nabajallah: Ƙasurgumin Ɗan Bindigan Katsina Ya Gamu Da Ajalinsa Sakamakon Rikicin Neman Aure

A wani labarin daban, rikici ya barke tsakanin bangarorin ƴan bindiga biyu masu adawa da juna a Katsina wadda ya yi sanadin mutuwar shugaban yan bindiga, Nabajallah, da wasu yan bindigan uku, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Sokoto: 'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma 11, Sun Kallafawa Wasu Harajin Noma

Majiyoyi sun ce an kashe shugaban yan bindiga, Dogo Nabajallah a cikin dajin Dungun Muazu da ke karamar hukumar Sabuwa a ranar Laraba.

A cewar rahoton Premium Times Hausa wasu ƴan bindigan da ke adawa da shi ne suka afka masa suka kashe shi saboda rikicin neman aure da ke tsakanin yaronsa da bangaren su yan adawan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel