Dogo Nabajallah: Ƙasurgumin Ɗan Bindigan Katsina Ya Gamu Da Ajalinsa Sakamakon Rikicin Neman Aure
- Mummunan rikici ya barke tsakanin bangarorin yan bindiga biyu a Katsina saboda wata mace
- Rikicin neman auren ya yi sanadin mutuwar kasurgumin dan bindigan Dogo Nabajallah
- Bangaren da ke adawa da Nabajallah ne suka kashe shi saboda yana goyon bayan yaronsa da ke gasar neman aure da su
Rikici ya barke tsakanin bangarorin ƴan bindiga biyu masu adawa da juna a Katsina wadda ya yi sanadin mutuwar shugaban yan bindiga, Nabajallah, da wasu yan bindigan uku, rahoton The Punch.
Majiyoyi sun ce an kashe shugaban yan bindiga, Dogo Nabajallah a cikin dajin Dungun Muazu da ke karamar hukumar Sabuwa a ranar Laraba.
A cewar rahoton Premium Times Hausa wasu ƴan bindigan da ke adawa da shi ne suka afka masa suka kashe shi saboda rikicin neman aure da ke tsakanin yaronsa da bangaren su yan adawan.
Wasu mazauna garin da suka nemi a ɓoye sunansu, sun ce ƴan bindigan ba su ji daɗin yadda Nabajallah ya ke katsalandan kan auren matar bane hakan yasa suka kai masa harin a ranar Laraba.
An kuma gano cewa yaran Nabajallah, wadanda suka fusata da kisarsa sun tafi ɗaukan fansa inda suka hallaka mutum uku ckin yan bangaren adawan.
Mutanen gari sun dakatar da zuwa gonakinsu
Wani mazaunin garin, a ranar Alhamis ya ce:
"Tunda aka kashe Nabajallah a jiya (Laraba), muna fargabar zuwa gona. Wasu daga cikin mu sun yanke shawarar cewa ba za mu tafi gonakin mu ba har sai tarzomar ta lafa. Babu wanda ya san abin da yan bindigan za su iya yi."
An gano cewar an birne gawar Nabajallah a cikin dajin a ranar Laraba.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, bai yi martani game da lamarin ba a lokacin hada wannan rahoton.
'Yan Bindiga Sun Sace Mata 13 a Hanyarsu Ta Zuwa Biki a Birnin Gwari
A wani labarin, yan bindiga sun sace mata 13 a tsakanin garuruwan Manini da Udawa da ke kan babban hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, a hanyarsu ta zuwa bikin daurin aure, Daily Trust ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis misalin karfe 12 na rana a lokacin da yan bindigan suka tare motocci uku da ke dauke da matan a hanyarsu ta zuwa Birnin Gwari.
An gano cewa cikin wadanda aka sace din akwai mata masu shayarwa da wata mata da yayanta mata biyar.
Asali: Legit.ng