Yakar 'yan bindiga: Hanyar da mazauna Zamfara za su bi su samu lasisin rike bindiga

Yakar 'yan bindiga: Hanyar da mazauna Zamfara za su bi su samu lasisin rike bindiga

  • Tun da farko gwamnatin jihar Zamfara ta umarci mazauna jihar da su dauki bindigogi domin kare kansu daga farmakin ‘yan bindiga
  • Hakan ya zama dole ne biyo bayan karuwar ayyukan ‘yan bindiga a sassan jihar cikin kwanakin nan, da irin barnar da suke yi
  • A wani sabon mataki, gwamnati ta bayyana yadda mutane za su iya samun lasisin bindiga tare da bin ka'idojin da ta gindaya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Punch ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta ce umarnin da ta bai wa mazauna kuma farar hula na mallakar bindigogi don kare kansu, ba wai ana nufin kowa ya mallaki bindiga ne sakaka ba.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

A Shirye Nake In Jagoranci Yaki da 'Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan Bauchi

Hanyar da za a bi wajen ba mutane bindiga a Zamfara
Yakar 'yan bindiga: Hanyar da mazauna Zamfara za su bi su samu lasisin rike bindiga | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Gwamna Matawalle ya goyi bayan bada lasisin bindiga

A sabon matakin da gwamnatin jihar ta dauka kan 'yan ta'adda, ta ce za ta aike da fam 500 na ba da lasisin mallakar bindiga ga masarautun jihar 19.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan zai ba da damar samar da lasisin bindigogi 9,500 kamar yadda gwamnati ta umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya ba da lasisin ga wasu mutanen da suka cancanta.

Sai dai, maganganu daban-daban a ranar Lahadi, 26 ga watan Yuni, sun biyo bayan umarnin, inda mazauna yankin da masana tsaro suka yi ta yabo wasu kuma kushewa tare da bayyana illar hakan.

Amma yayin da yake karin haske kan umarnin gwamnati, Dosara ya ce:

“Tsarin da muka kafa tsari ne mai tsafta. Mun fara da cewa a bar mutanen da ke son samun halaltattun makamai su zo su cike fom.

Kara karanta wannan

Kuma dai: Yan bindiga sun sake sace wani limamin Katolika a jihar Edo

“Sarakunan gargajiya za su bincike su tare da tantance su a yankunansu don tabbatar da cewa ba a ba wa wani mugun hannu ba ko kuma wani da ke da shaidar aikata laifi lasisin mallakar bindiga ba.
“Idan muka cike wadannan foma-foman, sai mu kai su wurin Kwamishinan ‘yan sanda don yin nasa binciken sannan kuma mu tantance mutanen kafin ya mika (bukatun) zuwa ga Sufeto-Janar na ‘yan sanda wanda daga karshe zai duba amincewa da bayar da lasisin."
"Don haka, muna bin doka da oda don tabbatar da cewa an bai wa mutanenmu halaltattun makamai don kare kansu."

'Yan bindiga sun sace sabon DPO a kan hanyarsa ta kama aiki a Kaduna

A wani labarin, an yi garkuwa da wani sabon jami’in ‘yan sanda (DPO) da aka tura zuwa Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

An sace DPO din ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da misalin karfe 9 na safe a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa ba Zamu Saki Nyame da Dariye ba Duk da Anyi Musu Rangwame, Hukumar Gidajen Gyaran Hali

Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa, DPO din na kan hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari ne domin kama aikinsa lokacin da aka sace shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.