Gwamnatin Yobe ta baiwa ma’aikata hutun kwanaki 3, ta bayyana dalili
- Gwamnatin jihar Yobe ta ayyana Laraba, Alhamis da Juma’a a matsayin ranakun hutu a fadin jihar
- Mai Mala Buni ya amince da hakan ne domin ba ma’aikatan gwamnati damar yin rijista, gyarawa da kuma karbar katunan zabensu
- Mukaddashin shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Bilal Garba, ya umarci daukacin ma’aikatan da su yi amfani da wannan karamci da aka yi masu yadda ya dace
Yobe - Gwamnatin jihar Yobe ta ayyana ranakun Laraba, Alhamis da Juma’a a matsayin hutu domin ba ma’aikatan gwamnati damar rijista da kuma karbar katunan zabensu, jaridar The Nation ta rahoto.
Sanarwar ta biyo bayan amincewa da hakan da Gwamnan Jihar Mai Mala Buni ya yi a wata takarda mai dauke da kwanan watan 27 ga watan Yuni mai lamba GO/S/HOS/GEN/3/T.II dauke da sa hannun mukaddashin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Alhaji Bilal Garba.
Premium Times ta nakalto Bilal yana cewa:
“Na rubuto wannan takardar ne domin na sanar da amincewar Gwamna Mai Mala Buni na ayyana gobe Laraba, Alhamis da Juma’a a matsayin ranakun hutun aiki don ma’aikatan gwamnati su samu damar zuwa kananan hukumominsu don yin rijista, gyarawa da kuma karbar katunan zabensu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Hakan ya kasance ne saboda muhimmancin da gwamnatin jihar ta baiwa rijistan masu zabe da ke gudana yanzu haka a fadin kasar.
“Ana fatan cewa ma’aikatan gwamnati za su yi amfani da wannan karamcin ta hanyar tabbatar da ganin cewa sun shiga tsarin."
Mukaddashin shugaban ma’aikatan ya bukaci dukkanin masu aiki mai muhimmanci a jihar da su kasance cikin shirin ko ta kwana.
A ranar Litinin ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da hukumar INEC daga kawo karshen yiwa masu zabe rijista a ranar 30 ga watan Yuni.
Justis Mobolaji Olajuwon na kotun ya bayar da umurnin ne na wucin gadi biyo bayan sauraron karar da kungiyar SERAP ta gabatar.
Zamu kara wa’adin rijistan katin zabe, Shugaban INEC
A gefe guda, hukumar shirya zaben kasa mai zaman kanta watao INEC ta bayyana cewa ba zata rufe kofar rijistan katin zabe ranar 30 ga Yuni, 2022 ba kamar yadda tsara.
Shugaban hukumar, Mahmoud Yakubu, ya bayyana hakan ranar Asabar yayin casun kira ga matasa su fito zabe a filin Old Parade Ground dame birnin tarayya Abuja, rahoton TheCable.
Yace:
“Abu na biyu shine yaushe za’a rufe rijista. A madadin INEC, ina mai tabbatar muku da cewa ba zamu rufe ranar 30 ga Yuni ba.”
Muddin kuna kokarin yin rijista ku mallaki PVC, zamu cigaba da muku rijista kuma zamu cigaba da kokarin ganin kun samu katin PVC.”
Asali: Legit.ng