Yanzu-yanzu: Zamu kara wa’adin rijistan katin zabe, Shugaban INEC

Yanzu-yanzu: Zamu kara wa’adin rijistan katin zabe, Shugaban INEC

  • Hukumar zabe ta INEC ta yi amai ta lashe, ta fasa rufe yin rijistar katin zabe karshen watan nan
  • INEC ta ce muddin yan Najeriya na cigaba da son yin rijista, ba za’a daina musu ba
  • Hukumar ta shirya casu na musamman don janyo hankalin matasa su tabbatar sun yi zabe

Abuja - Hukumar shirya zaben kasa mai zaman kanta watao INEC ta bayyana cewa ba zata rufe kofar rijistan katin zabe ranar 30 ga Yuni, 2022 ba kamar yadda tsara.

Shugaban hukumar, Mahmoud Yakubu, ya bayyana hakan ranar Asabar yayin casun kira ga matasa su fito zabe a filin Old Parade Ground dame birnin tarayya Abuja, rahoton TheCable.

Yace:

“Abu na biyu shine yaushe za’a rufe rijista. A madadin INEC, ina mai tabbatar muku da cewa ba zamu rufe ranar 30 ga Yuni ba.”

Kara karanta wannan

Bai Tsinana Mana Komai Ba: Matasa Da Mata Sun Huro Wuta A Karamar Hukuma, Sun Ce Dole A Tsige Ciyaman

Muddin kuna kokarin yin rijista ku mallaki PVC, zamu cigaba da muku rijista kuma zamu cigaba da kokarin ganin kun samu katin PVC.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

INEC chairperson
Yanzu-yanzu: Zamu kara wa’adin rijistan katin zabe, Shugaban INEC
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel