Yanzu-Yanzu: Jihar Zamfara Za Ta Fara Yanke Wa Masu Garkuwa Da Yan Bindiga Hukuncin Kisa
- Za a fara yanke wa masu garkuwa da mutane, yan bindiga da masu kai wa yan bindiga rahoto da taimaka musu hukuncin kisa a Jihar Zamfara
- Hakan na zuwa ne bayan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta amince da kudin dokar yanke hukuncin kisan da Gwamna Matawalle zai saka wa hannu a yau
- Gwamnatin na Zamfara ta yi wannan dokar ne da nufin magance matsalar yan bindiga da masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa da ya zama ruwan dare a jihar da wasu jihohin Najeriya
Zamfara - Abdullahi Shinkafi, mashawarci na musamman kan harkoki tsakanin hukumomin gwamnati ga gwamnan Zamfara, ya ce Majalisar Dokokin Jihar ta amince da kundin dokar hukuncin kisa ga yan bindiga, rahoton The Cable.
Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Matar Ciyaman Din NULGE Na Jihar Zamfara Da Cikin Wata 9
"Yau, gwamna zai rattaba hannu kan dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa, masu kai musu bayanai da sauran laifuka masu alaka da yan bindiga," in ji shi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Majalisar dokokin jihar, a jiya a Zamfara ta amince da dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, masu kai musu bayanai da masu basu gudunmawa."
Shinkafi ya ce umurnin 'harbi nan take' da Gwamna Bello Matawalle ya bada ba a kowanne yanki ne jihar bane ta ke aiki.
"Batun harbi nan take na aiki ne kawai a garin Mada da ke karamar hukumar Gusau, inda yan bindiga suka yi kaka-gida suna kai wa mutanen gari hare-haren," in ji shi.
Wannan umurnin na zuwa ne a lokacin da gwamnan ya bada umurnin cewa mutanen jihar su mallaki makamai don kare kansu daga harin yan bindiga.
Gwamnan ya kuma umurci rundunar yan sanda ta bada lasisin mallakar bindiga ga dukkan wadanda suka cancanta kuma suke son makamai don kare kansu.
Sai dai Rundunar Sojojin Najeriya da wasu kungiyoyi na arewa sun soki Wannan matakin na Gwamna Matawalle na karfafawa mazauna jihar gwiwa su mallaki makamai.
Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Matar Ciyaman Din NULGE Na Jihar Zamfara Da Cikin Wata 9
A wani rahoton, yan bindiga sun sace matar shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi, NULGE, ta Jihar Zamfara, Sanusi Mohammed Gusau.
Matar, Ramatu Yunusa, wacce ke da ciki na wata tara, an sace ta ne a gidan mijinta da ke Damba a Gusau, safiyar ranar Talata.
Asali: Legit.ng