Hotunan dan autan marigayi sarkin Kano Ado Bayero yayin da ya angwance da mata biyu a lokaci guda

Hotunan dan autan marigayi sarkin Kano Ado Bayero yayin da ya angwance da mata biyu a lokaci guda

  • Dan marigayi sarkin Kano, Mustapha Ado Bayero, ya angwance da kyawawan matayensa har su biyu
  • An daura auren Mustapha da matayen nasa, Fatima da Badi'a a yau Lahadi, 26 ga watan Yuni, a birnin Kano
  • Yariman wanda ya kasance dan autan marigayi sarkin ya yi shiga ta alfarma tare da rawani wanda ya nuna kwarjini irin na sarauta a tattare da shi

Kano - Mustapha Ado Bayero, dan autan marigayi sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya angwance da tsala-tsalan matansa guda biyu.

Dubban jama’a sun shaida daurin auren Mustapha Bayero a yau Lahadi, 26 ga watan Yuni, a birnin Kanon, sashin Hausa na BBC ta rahoto.

Autan sarkin Kano tare da matansa biyu
Hotunan dan autan marigayi sarkin Kano Ado Bayero yayin da ya angwance da mata biyu a lokaci guda Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

An kuma yi biki na alfarma da sarauta inda aka gano angon zaune a tsakanin amaren nasa masu suna Badi’a da Fatima.

Kara karanta wannan

Za a shirya wasan kwaikwayo a kan tarihin tsige Sanusi I da Sanusi II a 1963 da 2020

Mustapha ya kuma kasance sanye da alkyabba wacce ke nuna kwarjininsa na jinin babban gidan sarauta, sarautarma irin ta Kano.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amaren ma sun yi shiga iri daya yayin da kansu ke yane da mayafi. An kuma gano dogarawa zagaye da su.

Aure ya kullu: Bidiyoyi da hotuna daga shagalin bikin Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa Ummi Rahab

A wani labarin, mun ji cewa alkawarin Allah ya cika a tsakanin jarumi kuma fitaccen mawaki a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Shu'aibu Ahmed Idris, wanda aka fi sani da Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa, jaruma Ummi Rahab.

A ranar Asabar 18 ga watan Yuni, ne dubban jama’a suka shaida daurin auren manyan jaruman guda biyu.

An yi shagulgula da dama domin raya wannan rana inda amarya Ummi ta fito shar da ita saboda tsabar kyawu da haduwa.

Kara karanta wannan

Likafa ta ci gaba: Matan marigayi Alaafin na Oyo sun baje kolin sabbin gidajen da suka mallaka

Asali: Legit.ng

Online view pixel