Kaduna: Yan Sanda Sun Bindige Dan Ta'adda Har Lahira, Sun Kwato Bindiga Da Babur

Kaduna: Yan Sanda Sun Bindige Dan Ta'adda Har Lahira, Sun Kwato Bindiga Da Babur

  • Jaruman jami'an yan sandan Najeriya a Kaduna sun ragargaji yan bindiga sunyi nasarar kashe guda cikinsu a karamar hukumar Giwa
  • DSP Mohammed Jalige, mai magana da yawun yan sandan Jihar Kaduna ya sanar da hakan a ranar Alhamis 23 ga watan Yuni
  • Jalige ya kuma ce yan sandan sun yi nasarar kwato bindiga kirar AK-49 da babur guda daya da wani bindigan kirar gida Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kaduna - Yan Sanda a Jihar Kaduna sun bindige wani dan bindiga kuma suka kwato AK-49, da wata bindigar kirar gida Najeriya da babur guda daya a Kaduna.

Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis a lokacin da jami'an tsaro suka samu kirar neman dauki cewa an hangi yan bindiga a kan hanyar Galadimawa Kidandan a karamr hukumar Giwa.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun ceto wasu mutane 14 da aka yi garkuwa da su a dajin Zamfara

A cikin wata sanarwa, kakakin yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya ce tawagar yan bindigan ya janyo hankulan mutane, rahoton Daily Trust.

Hoton Mutum Da Kayan Soja.
An Bindige Wani Dan Ta'adda Sanye Da Kayan Sojoji A Kaduna
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Jami'an tsaro sun ragargaji yan bindigan suka dakile harin da suka yi niyyar kaiwa hakan yasa suka tsere suka koma daji da raunin bindiga yayin da aka bindige daya cikinsu har lahira, aka kwace bindigarsa AK-49 da babur," in ji shi.

Kwamishinan yan sandan Jihar Kaduna ya jinjinawa kokari da jajircewa na yan sandan jihar wurin tsare lafiya da dukiyoyin al'umma.

Ya kara da cewa su cigaba da kokarin ganin nasarorin da aka samu wurin kawo karshen bata gari ya cigaba.

'Yan Fashi Da Makami Sun Bindige Manjo Na Soja Har Lahira A Jigawa

A wani rahoton, Rundunar sojojin Nigeria ta bayyana cewa ƴan fashi da makami sun bindige muƙadasshin kwamandan 196 Battalion, Manjo MS Sama'ila a Dundubus, Jigawa, News Wire ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari birnin Katsina, sun yi garkuwa da mazauna yankin da dama

A cewar sanarwar da rundunar sojojin ta fitar a ranar Talata, an kashe Sama'ila ne misalin ƙarfe 11.30 na daren ranar Lahadi a hanyarsa ta zuwa Kano daga Maiduguri da mai tsaronsa Alisu Aliyu.

Yayin da an kai gawar Sama'ila asibitin ƙwararru ta Rashid Shekoni da ke Dutse, Aliyu wanda ya tsira da harbin bindiga yana samun kulawa a asibitin na Shekoni da ke Dutse kamar yadda News Wire ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel