Layukan Wayan Ekweremadu Da Na Kakakinsa A Kashe, Yayin Da Aka Kama Shi Da Matarsa A Landan

Layukan Wayan Ekweremadu Da Na Kakakinsa A Kashe, Yayin Da Aka Kama Shi Da Matarsa A Landan

  • An lalubi wayoyin salular tsohon mataimakin shugaban majalisa Sanata Ike Ekweremadu da kakakinsa ba a samu ba
  • Hakan na zuwa ne a lokacin da mahukunta a kasar Birtaniya suka sanar da kama wani mai suna irin na tsohon kakakin majalisar da matarsa kan zargin safarar sassan jikin bil adama
  • Yan sandan na Birnin Landan sun ce an garkame mutanen kuma za a gurfanar da su a gaban kotu a yau Alhamis

Layukan wayan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawar Najeriya, Ike Ekweremadu da na Ache Anichukwu, mai magana da yawunsa a halin yanzu suna kashe, Daily Trust ta rahoto.

A ranar Alhamis, yan sanda a Landan sun sanar da kama wasu mata da miji masu suna irin na tsohon kakakin majalisar dattawar na Najeriya Ike Ekweremadu da matar Beatrice Nwanneka Ekweremadu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun sako Sarkin da suka nemi Miliyan N150m fansa a jihar Arewa

Ike Ekeremadu.
Layukan Wayan Ekweremadu Da Na Kakakinsa A Kashe, Yayin Da Aka Kama Shi Da Matarsa A Landan. Hoto: @daily_trust.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta yi kokarin kiran mutane biyun ta wayar tarho amma layukansu ba su shiga.

A cikin sanarwar, Yan sandan Birnin Landan sun ce:

"An gurfanar da wata mata da miji a yau da laifin hadin baki don shirya tafiyar wani yaro zuwa Birtaniya don cire sassan jikinsa.
"An yi gurfanarwar ne sakamakon bincike da Yan sandan Birnin Landan na sashin laifuka na musamman suka yi.
"Beatrice Nwanneka Ekweremadu, 55 (10.9.66) na Najeriya ana tuhumarta da sufurin wani mutum da niyyar cire wani sashen jikinsa."
"Ike Ekweremadu, 55 (10.9.66) na Najeriya ana tuhumarsa da sufurin wani mutum da niyyar cire wani sashen jikinsa."
"An garkamesu kuma zasu gurfana gaban kotun Uxbridge yau."
"An kwace yaron hannunsu kuma ana kula da shi."

Ekweremadu, wanda ke da gida a Landan, a baya-bayan nan ba a ganinsa a majalisa na yan kwanaki.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari birnin Katsina, sun yi garkuwa da mazauna yankin da dama

A cikin ganin da aka masa a baya-bayan nan a Najeriya, ya ce duk da cewa Labour Party ta tsaya da Igbo a matsayin dan takara, Igbo za su zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na PDP.

Ekweremadu ya nuna sha'awar gadon Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu amma bai samu tikitin takara a PDP ba.

An damke Sanata Ekweremadu da matarsa kan yunkurin satar sashen jikin wani yaro

Tunda farko kun ji cewa hukumomi a kasar Birtaniya ta damke tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, da matarsa Beatrice kan laifin kai wani yaro kasar don cire wani sashen jikinsa.

Hukumar yan sandan kasar ta tabbatar da labarin cewa an garkamesu a kurkuku kuma za'a gurfanar da su a kotu ranar Alhamis bayan gudanar da bincike, rahoton Skynews.

Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da bincike ne bayan sanar da su wasu sun kawo dan wani kasar kuma hakan ya sabawa dokar bautar zamani na Birtaniya.

Kara karanta wannan

Za a shirya wasan kwaikwayo a kan tarihin tsige Sanusi I da Sanusi II a 1963 da 2020

Asali: Legit.ng

Online view pixel