Masu Garkuwa da Mutane Sun ci mu Tarar N1m Saboda Lattin Kai Kudin Fansa, Mata da Miji

Masu Garkuwa da Mutane Sun ci mu Tarar N1m Saboda Lattin Kai Kudin Fansa, Mata da Miji

  • Wasu ma'aurata da suka shaki iskar 'yanci bayan masu garkuwa da mutane sun sacesu, sun bayyana halin da suka tsinci kansu a sansanin miyagun
  • Kamar yadda Alhaji Tukur Turaki da matarsa suka bayyana, sun sasanta kan za a biya kudin fansa N10m amma lattin kai kudin yasa suka caje su karin N1m
  • Ya sanar da yadda rayuwa ta kasance abun tsoro a sansanin 'yan bindigan da suka yi niyyar halaka shi da farko

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Wasu mutum biyu da kwanan nan aka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina, mata da miji, sun bayyana cewa sai da suka biya miliyan 11 sannan aka sako su.

Idan za mu tuna, kwanaki 10 da suka gabata, 'yan bindiga sun kai farmaki yankin Shola dake karamar Hukumar Katsina ta jihar Katsina inda suka sace mutum shida.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30

Masu Garkuwa da Mutane
Masu Garkuwa da Mutane Sun ci mu Tarar N1m Saboda Lattin Kai Kudin Fansa, Mata da Miji. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daya daga cikinsu wadanda aka sacen mai suna Alhaji Tukur Turaki, yace a wannan daren, matarsa ta ji wasu mutane suna dukan dan su kuma ta yi zaton sojoji ne, don haka sai ta bude kofar gida wanda hakan ya bai wa masu garkuwa da mutanen damar shigowa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A lokacin da suka shigo, sun tambaya matata inda nake kuma kafin ta nuna inda nake, na amsa su. Sun tambaye mu kudi kuma na basu N700,000 da nake da ita.
"Bayan karbar kudin, daya daga cikinsu ya ce ba kudi ya kawo su ba, kawai an yi hayarsu ne su kashe ni. Sai nace masa ya fada min yadda zan tsaya ya kashe ni. Da yaji haka, sai ya rike hannuna yace ba za mu kashe ka ba, amma za mu tafi da kai ta yadda sai ka biya kudin fansa ka fanshi kanka.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari Kaduna, sun sace mutane 36

"A lokacin da muka fita waje, matata ta biyo ni amma sai suka ce ta koma. Daya daga cikinsu sai yace ta biyo mu, a haka ita ma aka yi garkuwa da ita," ya tuna.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, yace sun yi doguwar tafiya har zuwa kauyen Bugaje dake karamar Hukumar Jibia inda 'yan bindigan suka ajiye baburansu, suka dauka sannan suka sake shiga dakin.

"Washegari, sun bukaci kudin fansa har N30 miliyan daga wurina amma sai muka sasanta a N10 miliyan. An yi ruwa ranar, hakan yasa ba a kawo kudin ba sai washegari. Daga nan wadanda suka sace mu suka ce sai mun kara musu N1 miliyan na jinkirin kwana daya. Haka na kira 'yan uwa suka ciko miliyan dayan," yace.

Turaki ya kwatanta rayuwa a wurin da abu mai tsoratarwa inda yace daya daga cikin wadanda aka sace tana da karamin yaro wanda ake masa amfani da leda a matsayin famfas. Yace ba a yi wa yaron wanka ba a iya kwanakin da suka yi.

Kara karanta wannan

Yadda Ango Ya Sheka Barzahu a Kokarin Hana 'Yan Bindiga Sace Matarsa Mai Ciki

A bangaren ta, Sa'adatu Turaki tace 'yan bindigan sun sace wasu har da mai jego a kwatas din Shola.

"Lokacin da na gane mai jegon na fama da matsalar numfashi, na karba jaririn tare da goya shi. Mun je wani wuri inda suka raba N700,000 a tsakaninsu," tace.

Hajjin Bana: Maniyyatan da aka yi Garkuwa dasu a Sokoto Sun Samu 'Yanci

A wani labari na daban, an ceto maniyyatan hajjin bana na jihar Sakkwoto bayan sun dauki awanni a hannun 'yan bindigan da suka yi garkuwa dasu a sa'o'in farko na ranar Talata, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kamar yadda takardar da gwamnatin jiha ta fitar wanda mai bada shawara ta musamman a lamurran da suka shafi yanar gizo Bello Muhammad ya bayyanawa manema labaran jihar Sakkwoto, an ceto maniyyatan hajjin banan cikin koshin lafiya ba tare da wani abu ya samesu ba.

Maniyyatan hajjin bana sun kai su 21 wandanda ke kan hanyarsu zuwa Sakkwoto, daga karamar hukumar Isa zuwa babban birnin jihar don su hau jirgin zuwa masarautar Saudi don yin aikin Hajjin shekarar 2022 yayin da 'yan bindiga suka bude musu wuta tare da yin awon gaba dasu na tsawon awanni.

Kara karanta wannan

ISWAP Ta Halaka Rayuka 16, Ta yi Garkuwa da Ma'aikatan Tallafi 3 a Borno

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng