INEC ta mika wa zababben gwamnan Ekiti, Oyebanji da mataimakinsa takardar shaidar lashe zabe
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta gabatar da takardar cin zabe ga zababben gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji da mataimakinsa Monisade Afuye
- Oyebanji ne ya lashe zaben gwamnan Ekiti da aka yi a ranar Asabar, 18 ga watan Yuni bayan ya lallasa abokan hamayyarsa
- Kwamishinan zabe na kasa da ke kula da jihar, Sam Olumekun, ne ya mika masu takardar inda ya nuna gamsuwa da yadda aka yi zaben
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Ekiti - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta gabatarwa zababben gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji da mataimakinsa, Monisade Afuye takardar shaidar cin zabe.
A ranar Asabar, 18 ga watan Yuni ne aka gudanar da zaben gwamnan a fadin jihar Ekiti.
Da yake gabatar masu da takardar a Ado Ekiti, babban birnin jihar, kwamishinan zabe na kasa da ke kula da jihar, Sam Olumekun, ya nuna gamsuwa kan yadda aka gudanar da zaben, Channels tv ta rahoto.
Olumekun ya kuma yaba da rawar ganin da fasaha ya taka a zaben.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake jawabi, zababben gwamnan, Oyebanji ya yabawa INEC da hukumomin tsaro a kan namijin kokarin da suka yi.
Ya kuma danganta nasarar da ya samu a zaben da ayyukan Gwamna Kayode Fayemi, inda ya yi alkawarin daurawa daga inda ya tsaya.
A ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni ne aka ayyana Oyebanji a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya kayar da manyan abokan hamayyarsa na jam’iyyun Social Democratic Party (SDP) da Peoples Democratic Party (PDP).
Jaridar The Cable ya rahoto cewa Bisi matar Gwamna Kayode Fayemi da matar zababben gwamnan, Olayemi Oyebanji duk sun halarci taron.
Zababben gwamnan Ekiti Biodun Oyebanji ya yi godiya ga al’ummar jiharsa
A gefe guda, mun ji a baya cewa kasa da sa’o’i 12 bayan hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya saki jawabinsa na farko.
Oyebanji ya saki jawabin nasa ne a takaice a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni, jim kadan bayan sanar da shi a matsayin zababben gwamnan na jihar Ekiti.
Sabon gwamnan wanda ya kasance dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya yi godiya ga daukacin al’ummar jihar Ekiti da suka zabe shi har ya kai ga lashe zaben na ranar Asabar, 18 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng