Da Duminsa: Hukumar INEC ta Kara Wa'adin Rijistar Katin Zabe
- Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasa, INEC, ta amince da kara wa'adin rijistar katin zabe a fadin kasar nan
- Da farko dai, majalisar wakilai ta bukaci INEC da ta kara wa'adin wanda tace zai cika a ranar 30 ga watan Yunin 2022
- A halin yanzu, an kara kwanaki 60 kan wa'adin farko kuma majalisar ta bukaci INEC da ta kara yawan ma'aikata da injinan aiki
FCT, Abuja - Hukumar Zabe mai zaman kanta, INEC, ta amince da tsawaita wa'adin rijistar katin zabe da ake yi wanda a baya tace za a gama shi a karshen watan Yunin 2022.
Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan lamurran zabe, Honarabul Aishatu Jibril Dukku, ta bayyana hakan yayin jawabi ga sauran 'yan majalisar kan kokarin kwamitin wurin tabbatar da hukuncin da suka yanke makon da ya gabata.
"Kwamitin yayi taro da INEC jiya Talata kuma sun amince da kara wa'adin rijistar katin zabe da sauran bukatun da muka mika musu duk sun amince," ta sanar da mambobin majalisar a ranar Laraba.
A ranar Laraba da ta gabata ne majalisar wakilan ta yi kira ga INEC da su kara wa'adin rijistar katin zabe da kwanaki 60 bayan ranar 30 ga watan Yunin 2022, domin bai wa 'yan Najeriya damar rijista.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar ta yi kira ga hukumar da ta kara ma'aikata da kuma injinan yin katin zaben a fadin kasar nan domin a cimma manufa, Leadership ta ruwaito.
Shugaban kwamitin yada labarai da hulda da jama'a na majalisar, Honarabul Benjamin Kalu, ya ce da farko za a kammala rijistar katin zaben kamar yadda hukumar tace a ranar 30 ga watan Yunin 2022 kafin zuwan zaben 2023.
Kotu ta dakatar da INEC daga rufe rijistar katin zaɓe a Najeriya
A wani labari na daban, babbar Kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC daga rufe rijistar Katin Zaɓe a ranar 30 ga watan Yuni, 2022.
The Cable ta ruwaito cewa hukumar INEC ta zaɓi ranar 30 ga watan Yuni a matsayin ranar da zata rufe damar yin Katin zaɓe (CVR) yayin da take shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2023.
Alƙalin Kotun, Mai Shari'a Mobolaji Olajuwon, ya amince da hukuncin biyo bayan sauraron buƙatun ƙungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP).
Asali: Legit.ng