Sabon hari: Mutum 10 sun mutu, 5 sun hallaka a harin 'yan ta'adda a jihar Benue

Sabon hari: Mutum 10 sun mutu, 5 sun hallaka a harin 'yan ta'adda a jihar Benue

  • Yan bindiga sun kai sabon farmaki kan al’ummar karamar hukumar Guma da ke jihar Benue a yammacin ranar Litinin
  • Maharan sun kai harin ne a kan wasu dilallan katakai a hanyarsu ta dawowa daga jeji inda suka yanko bishiyoyi
  • Zuwa yanzu an gano gawarwakin mutum biyar daga cikinsu yayin da aka nemi sauran mutane 10 aka rasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Benue - Akalla gawarwakin mutane biyar aka gano a ranar Talata, 21 ga watan Yuni, bayan wasu yan ta’adda sun kaddamar da sabon hari a kan al’ummar karamar hukumar Guma da ke jihar Benue.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutane 10 sun bata yayin da aka tura wata tawaga domin kakkabe dazuzzuka tare da binciko inda suke.

Shugaban karamar hukumar Guma, Caleb Aba, a wata hira ta wayar tarho ya bayyana cewa lamarin ya afku ne a yammacin ranar Litinin a garin Mbagwen amma an sanar masa a ranar Talata da rana.

Kara karanta wannan

Borno: An Fallasa Dabarju, Mai Tatsar Wutar Fitillun Kan Titi Yana Kaiwa Gidan Kankararsa

Yan bindiga
Sabon hari: Mutum 10 sun mutu, 5 sun hallaka a harin 'yan ta'adda a jihar Benue Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Aba ya ce wadanda lamarin ya ritsa da su sun kasance dillalan katakai wadanda suka je kwaso bishiyoyin da suka yanka a dajin Mbagwen, wani gari da ke kusa da Yelewata a Guma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar ta nakalto Aba yana cewa:

“Lamarin ya afku ne a yammacin jiya Litinin lokacin da wasu dilallan katakai suka je jeji kwaso itatuwansu.
“Sun kwaso katakan a kan hanyarsu ta dawowa ne aka farmake su. Su 15 ne.”
“Zuwa yanzu an gano gawarwaki biyar. Har yanzu ba a ga sauran mutane 10 ba. Bamu sani ba ko an kashe su ko kuma an yi awon gaba da su ne, ana kan nemansu a yanzu haka da muke magana.”

Kakakin yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta bayyana cewa bata da masaniya kan lamarin, inda ta ce tana halartan wani taron karawa juna sani a wajen jihar.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: ‘Yan bindiga sun tare Maniyyata a hanyar filin jirgi, su na shirin zuwa Saudi

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun sako tsohon Sakataren Hukumar NFF, Sani Toro da wasu 2

A wani labarin, rundunar yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da sakin tsohon sakataren Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya (NFF), Sani Toro, tsohon mataimakin kocin Super Eagles, Garba Yila da Alhaji Isa Jah.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rahoto cewa rundunar yan sandan ta ce yan bindiga da suka yi garkuwa da su ne suka sako su.

Kakakin yan sandan, Sp Ahmed Wakil, wanda ya tabbatar da sakin nasu ga manema labarai a jihar Bauchi a ranar Talata, 21 ga watan Yuni, ya ce babu cikakken bayani kan yadda aka sake su a yanzu haka, jaridar The Sun ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng