Karfin hali: ‘Yan sanda sun cafke wasu mutane 6 da ake zargin ‘yan fashin banki ne
- Rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta yi nasarar kame wasu da ake zargin 'yan fashin banki ne a wani yankin jihar
- Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, daga cikin 'yan fashin, an kama wani matashi da ma'aikacin bankin ne
- Ya zuwa yanzu, rundunar ta ce tana ci gaba da bincike don tabbatar da wadanda ake zargin ba su tsira ba
Ibadan Jihar Oyo - Rundunar ‘yan sanda a jihar Oyo ta cafke wasu mutane shida da ake zargin 'yan wani gungun barayin banki ne.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso ne ya bayyana haka a garin Ibadan a ranar Litinin, inda ya ce daga cikin wadanda ake zargin akwai wani ma’aikacin kwantiragi mai shekaru 29 da haihuwa na bankin,
Rahoton jaridar Daily Sun ta ce, daya daga cikin wadanda ake zargin mace ce.
Ya kara da cewa, an kama wadanda ake zargin ne a maboyar su da ke Agara, Unguwar Odo-Ona a Ibadan a ranar 13 ga watan Yuni bayan sun kammala shirin yin fashin wani banki a washegari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Osifeso ya kuma bayyana cewa wadanda ake zargin sun amsa laifinsu da aikata laifuka daban-daban da suka hada da sayan makamai da kuma tattara bayanan sirri a boye a gabanin fashin.
Ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike domin zakulo sauran ‘yan tawagar.
Da yake kira ga al'ummar jihar, ya ce:
“Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta bukaci al’ummar jihar Oyo da su ci gaba da hada kai da ‘yan sanda ta hanyar samar da bayanai masu inganci a kan lokaci don dakile miyagun laifuka da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar.”
An farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa, Tinubu a jiharsa Legas
Wani rahoton, a ranar Lahadi ne wasu ‘yan daba suka far ma motar bas din da ke dauke da ma’aikatan ofishin gwamnan jihar Legas a tsakanin Ebute-Ero da Adeniji, na yankin Iga-Iduganran a Legas, inda ‘yan jarida akalla biyu suka samu raunuka, wasu kuma suka kuje a jikinsu.
'Yan daba sun afkawa 'yan jaridan ne da ke cikin ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Tribune Online ta ruwaito.
An rahoto cewa, tsagerun sun kuma jefi motocin da ke cikin ayarin da ya kunshi jiga-jigan siyasa ciki har da Gwamna Babajide Sanwo-Olu; Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje; da sauran wadanda suka bar fadar Oba na Legas, Oba Rilwanu Akiolu.
Asali: Legit.ng