An ceto matar jigon APC da aka yi garkuwa da ita a Minna a tashar motar Kano da ke Maiduguri

An ceto matar jigon APC da aka yi garkuwa da ita a Minna a tashar motar Kano da ke Maiduguri

  • Rundunar yan sandan jihar Borno ta ceto Habiba Baffa, matar shugaban APC a yankin Makama ta jihar Neja, Usman Baffa
  • Wasu yan bindiga ne suka sace Habiba a garin Minna, babbar birnin jihar a ranar Lahadi amma sai aka tsince ta a Maiduguri, jihar Borno
  • Matar ta bayyana cewa mijinta maharan suka zo sacewa amma da basu same shi a gida ba sai suka yi awon gaba da ita

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an ceto matar Usman Baffa, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), na karamar hukumar Magama da ke jihar Neja, Habiba Baffa, wacce aka yi garkuwa da ita.

An dai yi garkuwa da Habiba ne a ranar Lahadi, a garin Minna, babbar birnin jihar Neja amma kuma an gano ta ne a shahararriyar tashar motar nan ta Kano da ke jihar Borno.

Kara karanta wannan

Okowa: Muhimman abubuwa 12 da baku sani ba game da abokin takarar Atiku a PDP

Kwamishinan yan sandan jihar Borno, Mista Abdu Umar, ne ya mika Misis Baffa ga iyalanta a Maiduguri a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuni, PM News ta rahoto.

Jami'an yan sanda rike da bindigogi
An ceto matar jigon APC da aka yi garkuwa da ita a Minna a tashar motar Kano da ke Maiduguri Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Da yake jawabin yayin mika ta, kwamishinan yan sandan ya ce shugaban kungiyar ma’aikatan sufuri na kasa a Maiduguri ya kai rahoto ofishin yan sanda a ranar Laraba cewa an tsinci wata mata mai suna Habiba Baffa a tashar mota ta Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Umar ya kara da cewar an ceto Misis Baffa sannan aka kaita ofishin rundunar inda bincike ya nuna cewa wasu yan bindiga hudu ne suka sace ta daga gidanta a yankin Tunga da ke Minna, babbar birnin jihar Neja, a ranar Lahadi kawai sai ta tsinci kanta a Borno.

Kwamishinan yan sandan ya bayyana cewa an tuntubi mijin matar da taimakon ta inda ya zo daga Neja domin sake haduwa da matar tasa.

Kara karanta wannan

Ana kishin-kishin, Tinubu ya nuna wanda yake so ya zama Mataimakinsa a zaben 2023

Umar ya ce:

“Shugaban kungiyar sufurin hanya na kasa ya janyo hankalin jami’an rundunar a ranar Laraba da misalin karfe 14:00, cewa an tsinci wata mata mai suna Habiba Baffa a tashar mota na Kano.”

Matar ta bayyana halin da ta tsinci kanta a ciki

Da take zantawa da manema labarai, Habiba ta bayyana cewa yan bindigar sun farmaki gidanta da misalin karfe 5:00am sannan suka tambayi ina mijinta.

Ta ce sun kuma bukaci makudan kudi wanda ta basu.

“Daga bisani sai suka nemi na shiga motarsu sannan suka tafi da ni. Kawai na farka ne na gano cewa ina Borno.”

Mijinta ya yi martani

Jaridar ta kuma rahoto cewa da yake martani, Baffa ya yi godiya ga Allah cewa an ceto matarsa kuma ya yabama rundunar yan sandan Najeriya kan kokarinsu.

Baffa ya ce:

“Ni aka so sacewa, amma tunda basu ganni ba, sai suka tafi da matata.

Kara karanta wannan

Yadda wasu ma’aikatan gidan gona a Abuja suka kashe ubangidansu, suka jefa gawarsa a cikin rijiya

“Na kasa bacci ko cin abinci, na shiga damuwa sosai. Ba zan iya tunanin rayuwa babu matata ba.”

Yan Bindiga Sun Bi Tsohon Kwamishina Har Gidansa Sun Sace Shi a Adamawa, Sun Bindige Mutum 2 Har Lahira

A wani labarin, mun ji cewa wasu yan bindiga sun sace tsohon kwamishinan Gidaje da Tsara Birane, Injiniya Babangida a gidansa da ke Adamawa a ranar Talata.

An rahoto cewa wadanda suka sace shi sun zagaye gidansa da ke kauyen Bajabire a karamar hukumar Girei na jihar sannan suka harbe shi a kafa, Daily Trust ta rahoto.

Yan bindigan sun kuma kashe wasu mutane biyu sun kuma raunata wasu da dama kafin suka sace tsohon kwamishinan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng