2023: Bishop Ya Gargadi Kirista Kan Abin Da Zai Biyo Baya Idan Musulmi 2 Suka Zama Shugaban Kasa Da Mataimaki
- Babban malamin addinin kirista, Bishop Paul Nwachukwu ya gargadi kiristoci kan abin da zai faru idan musulmi suka zama shugaban kasa da mataimaki
- Bishop Nwachukwu ya ce muddin musulmi biyu suka zama shugaban kasa da mataimaki a Najeriya, kirista ba za su samu kulawa a kasar ba
- Malamin addinin ya shawarci kiristoci na Najeriya su tabbatar sun mallaki katin zabe sannan su shiga harkar zaben a dama da su don zaben shugabanni a 2023
Shugaban Cocin 'Grace of God Mission International', Bishop Paul Nwachukwu, ya ce kirista ba za su amince da musulmi su zama shugaban kasa da mataimaki ba a zaben 2023.
Nwachukwu ya ce manyan jam'iyyun siyasar kasar sun zabi musulmi a matsayin yan takarar shugaban kasa amma su tuna cewa Najeriya ba kasar musulunci bane, rahoton The Punch.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce zaben musulmi a matsayin mataimakansu zai janyo kiristoci su dena samun kulawa a kasar kamar yadda Nigerian Tribune ta rahoto.
A wani sako da ya fitar mai taken 'The battle I will like to lose’, malamin addinin ya ce:
"Ina son yan siyasa su tuna cewa Najeriya ba kasa ce ta wani addini guda ba, don haka yayin zaben mataimakansu, su sani ba za a amince da wani musulmi ba.
"Najeriya tamu ce baki daya, kuma dukkan yankunan kasar da addinan na da muhimmanci. Zaben musulmi a matsayin yan takararsu zai zama rashin kulawa ga kiristoci," in ji Nwachukwu.
Yayin da jam'iyyar PDP ta zabe Atiku, musulmi daga arewa a matsayin dan takarar shugaban kasa, jam'iyyar APC mai mulki ta zabi musulmi daga kudu, Bola Tinubu.
Bishop Nwachukwu ya shawarci kiristoci su tabbatar sun mallaki PVC
Bishop din ya zaburar da kiristocin Najeriya su tabbatar sun mallaki katin zabe wato PVC, yana mai cewa wannan ba lokacin zama bane, don haka su shiga harkar zabe a dama da su.
Ya ce hanya daya da za a iya samun damar zaben wanda zai zama shugaba a kasa shine ta hanyar yin rajistan zabe da jefa kuri'a.
Ya kuma yi kira ga INEC ta saukaka hanyoyin yin rajistan duba da cewa masu zabe kansu ya kara waye wa kuma a shirye suke su yi zaben.
Tsohon Hadimin Buhari Ya Ragargaji Peter Obi, Ya Bayyana Abin Da Yasa Tsohon Jigon Na PDP Ya Koma Labour Party
A wani rahoton kun ji cewa an yi yakin baka tsakanin Ahmad Bashir, tsohon hadimin Shugaba Muhammadu Buhari a bangaren sabon kafar watsa labarai da jam'iyyar Labour Party, LP, da dan takarar shugaban kasarta, Peter Obi.
Amma, bisa alamu Ahmad ya fi sakin zafafan kalamai inda yayin kambama kansa ya yi ikirarin Obi ya fice daga jam'iyyar PDP ne don yana tsoron ba zai samu kuri'a ko daya ba a zaben fidda gwani na PDP.
Asali: Legit.ng