Malamin addini: Ba a taba mulkin 'yan rashawa kamar na Buhari ba a tarihin Najeriya

Malamin addini: Ba a taba mulkin 'yan rashawa kamar na Buhari ba a tarihin Najeriya

  • Babban malamin addini a cocin Living Faith ya caccaki gwamnatin Buhari, inda yace babu gwamnati mafi muni kamar tasa
  • Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gudanar da wani karatu a cocinsa, kamar yadda rahotanni suka shaida
  • Ya kuma bayyana cewa, da gangan gwamnatin ta ki biyan bukatar ASUU, ganin kankantar kudin da suke bukata

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Shugaban cocin Living Faith Church Worldwide, Bishop David Oyedepo, ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya bayyana ta a matsayin wadda tafi kowacce cin hanci da rashawa a tarihin Najeriya.

Da yake jawabi a wani shiri na baya-bayan nan a cocin sa, Oyedepo ya koka da irin halin kuncin da kasar ke ciki, inda ya danganta hakan da cin hanci da rashawa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Takarar Musulmi da musulmi: Ana yiwa Tinubu zagon kasa ne, in ji wani fasto

Fasto Ayedepo ya kwance gwamnatin Buhari
Malamin addini: Ba a taba mulkin 'yan rashawa kamar na Buhari ba a tarihin Najeriya | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce Naira biliyan 80 da ake zargin Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris ya sace, za su isa su biya bukatun kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, wanda ya kai ga rufe makarantu.

A wani bangare na kalamansa, ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mene ne yaki da cin hanci da rashawa? An yaudare ku duka. Ba za ku kasance cikin cin hanci da rashawa ba kuma ku ce kuna yaki da cin hanci da rashawa ba. Mulki mafi cin hanci da rashawa a tarihin Najeriya.
“Kun ji labarin babban mai binciken kudi... Naira biliyan 80. Duk abin da suke bukata don bude jami’ar bai kai Naira biliyan 80 ba amma ba su da sha’awar ba da wa saboda ‘ya’yansu ba sa nan."

Damfarar N80bn: ASUU ta zunɗi AGF, ta ce FG ta yi watsi da tsarin IPPIS

A ranar Talata, kungiyar malaman jami'a masu koyarwa (ASUU) ta bukaci gwamnatin tarayya da tayi watsi da tsarin biyan ma'aikata na IPPIS da take amfani dashi wajen biyan ma'aikatan tarayya albashi.

Kara karanta wannan

A kullum ina rayuwa cikin bakin ciki da damuwa saboda matsalar tsaro - Buhari

ASUU ta yi martani game da cafke akawu janar na tarayya, Ahmad Idris da hukumar EFCC tayi bisa zarginsa da almundahana, tare da sunkuce N80 biliyan jaridar Newswire ta ruwaito.

Shugaban ASUU, farfesa Emmanuel Osodeke, a wata tattaunawa da Daily Trust a jiya, ya ja kunne kan kada a yi rufa-rufa a lamarin, inda ya ce "mutanen banza sun cancanci horo duba da manufar wannan mulkin."

A wani labarin kuma, ASUU ta zargi jiga-jigan siyasar Najeriya da kwashe kudaden Najeriya gabanin babban zaben 2023 maimakon magance matsalolin da ke addabar ilimi a kasar.

Shugaban kungiyar ASUU, reshen jami’ar Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole ne ya bayyana hakan, inda ya kara da cewa gwamnati ta koma tattaunawa da kungiyar duk da cewa sabanin yarjajeniyar farko ne, rahoton Leadership.

A cewarsa, gwamnati da ASUU za su duba daftarin yarjejeniyar 2009 ta ASUU/FGN wacce tawagar gwamnati ta fara tare da ASUU a 2007 kuma aka kammala shi a watan Mayu, 2021.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Da Barayin Gwamnati Ke Boye Kudadensu a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.