Jigawa: Kotu ta daure masu garkuwa da mutane tsawon shekaru 28 bisa sace yarinya

Jigawa: Kotu ta daure masu garkuwa da mutane tsawon shekaru 28 bisa sace yarinya

  • Wata kotu a jihar Jigawa ta yankewa wasu mutane da suka aikata laifin garkuwa a wani yankin jihar
  • Hakazalika, an yankewa wani matrashi hukuncin kisan kai ta hanyar rataya bisa laifin kisan kai a wani yankin
  • Ana ci gaba da samun rikice-rikicen sace mutane tare da kisan kai a sassa daban-daban na Najeriya

Jigawa - Babbar Kotun Jihar Jigawa mai zamanta ta a Dutse, babban birnin jihar ta yanke wa wasu masu garkuwa da mutane uku hukuncin daurin shekaru 28 da watanni biyar a gidan yari ba tare da zabin tara ba.

An samu wadanda ake tuhumar da laifin yin kutse, hada baki da kuma sace wata yarinya mai suna Fatima Abdirrahman, dake karamar hukumar Taura ta jihar, inji Leadership.

Kara karanta wannan

Jerin mutane 50 da Bola Tinubu ya fito da su a siyasa har Duniya ta san da zamansu yau

Kotu ta daure mai gakurwa da mutane
Jigawa: Kotu ta daure masu garkuwa da mutane a magarkama tsawon shekaru 28 | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Da yake jawabi yayin yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai shari’a M.A Abubakar, ya ce bayan gabatar da shaidu uku ta bakin lauya mai shigar da kara, kotun ta gamsu da cewa babu shakka wadanda ake zargin sun aikata laifin.

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wadanda ake zargin sun aikata laifin hada baki, zagon kasa, da kuma yin garkuwa wanda ya sabawa sashe na 272 karamin sashe na 273 na kundin laifuffuka na jihar Jigawa.
“Bayan samun Musa Garba na karamar hukumar Ringim, Isah Sule Wangara na karamar hukumar Dutse da Shu’aibu Haruna na karamar hukumar Taura da aikata wadannan laifuka, kotun ta yanke musu hukuncin daurin shekaru 28 da watanni biyar a gidan yari.”

Kotu ta yankewa wani hukucin kisa ta hanyar rataya

Hakazalika, wata babbar kotun jihar Jigawa dake zamanta a karamar hukumar Birninkudu ta jihar ta yankewa wani matashi mai suna Zubairu Idris dan shekaru 30 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin aikata laifin kisan kai.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare

An gurfanar da Zubairu a gaban kotu a ranar 11 ga watan Oktoba, 2017 kan zargin daba wa wani Abubakar Abubakar wuka a kauyen Baji.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai shari’a Musa Ubale, ya ce an samu wanda ake zargin da laifin kisan kai wanda ya sabawa sashe na 221 (B) na kundin laifuffuka na Jigawa.

A cewar alkalin yayin hukunci:

“Kotu ta samu Idris da laifin kisan kai, don haka an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya."

An cafke mutumin da ya tada hankalin jama'a da ikrarin Boko Haram sun shigo gari

A wani labarin, Daily Trust ta rahoto cewa, rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta cafke wani mutum mai suna Wakilu Ogundairo bisa zarginsa da tayar da hankalin jama'a da cewa kungiyar Boko Haram ta farmaki garin Imosan-Ijebu da ke karamar hukumar Ijebu-Ode a jihar.

Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, ya ce wanda ake zargin ya yi ikrari a sakon murya ta Whatsapp da aka yada ga jama’a kan wannan lamari.

Kara karanta wannan

Saura kiris a yi garkuwa da gawar Deleget din Jigawa da ya mutu a taron APC

Ogundairo ya yi ikirarin cewa maharan na dauke da makamai, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin mazauna yankin da kuma kewayensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.