Basaraken da ‘Yan bindiga suka dauke a Kaduna ya tsira, ya shafe kusan kwanaki 40 a jeji
- Mai unguwan Rijana, Ayuba Dodo Dakolo da aka dauke kwanakin baya a gonarsa ya samu ‘yanci
- Ana tunani ‘yanuwan Ayuba Dodo Dakolo sun biya Naira miliyan 3 kafin ‘yan bindigan su sake shi
- Sai da ‘yanuwan wadanda aka dauke su ka kai wa ‘yan bindigan sigari, tayoyi da katin yin waya
Kaduna - Miyagun ‘yan bindigan da suka yi awon gaba da Mai unguwan Rijana, Ayuba Dodo Dakolo, sun fito da shi bayan an biya su kudin fansa.
Daily Trust ta fitar da rahoto a safiyar Juma’a cewa Ayuba Dodo Dakolo ya samu ‘yanci ne a ranar Litinin tare da mutum biyu da aka yi garkuwa da su tare.
‘Yanuwan wadannan Bayin Allah sun bada kudi, babura, wayoyin salula kafin su iya ceto su.
Wani ‘danuwan wadanda aka dauke ya bada labarin abin da ya faru, ya takaita maganarsa domin ‘yan bindiga sun ja kunnensu kan magana da ‘yan jarida.
“An yi tsawon kwanaki 39 ana tattaunawa kafin su fito da su. Duk su na cikin koshin lafiya, amma abin babu sauki.”
- 'Danuwan wanda aka dauke
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar ta ce an dauke Ayuba Dodo Dakolo ne a gonarsa da ke wani kauye da ake kira Kurmi a kusa da garin Chikwale, karamar hukumar Kachia, Kaduna.
Daga cikin abubuwan da masu garkuwa da mutanen suka bukata daga ‘yanuwan Mai martaban har da babura, fetur, man juye, tayoyi, sigari da katin waya.
‘Yanuwa da abokan arziki sun kai wa ‘yan bindigan wadannan kaya da suka bukaci a kawo masu.
Dakolo ya tabbatarwa Daily Trust cewa ya kubuta daga hannun ‘yan bindigan. Dakolo yace sai da ya saida bangaren gonarsa kafin ya iya biyan kudin fansa.
‘Yan bindigan sun karbi babura kirar Honda da wayoyin zamani da kudi masu yawan gaske.
Wata majiya ta ce sai da aka biya kimanin N3m sannan Mai unguwan ya dawo gida. An sake shi ne a wani gari kusa da Buruku a yankin dajin Birnin Gwari.
An dauke Mahaifiyar Zaura
A farkon makon nan aka samu labari ‘yan bindiga sun sace tsohuwar AA Zaura a gidan ta cikin tsakar dare a kauyen Zaura da ke karamar hukumar Ungogo.
Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya shaida cewa sun tura dakarun a ceto ta, kuma an yi nasarar yin hakan daga baya.
Asali: Legit.ng