Rundunar yan sanda ta karyata batun kai harin ramuwar gayya kan al’ummar Hausawa a Ondo

Rundunar yan sanda ta karyata batun kai harin ramuwar gayya kan al’ummar Hausawa a Ondo

  • Rundunar yan sandan jihar Ondo ta karyata rahotannin cewa an kai harin ramuwar gayya kan al'ummar Hausawa da ke yankin Sabo da ke jihar Ondo
  • Mai magana da yawun yan sandan jihar, Funmilayo odunlami, ta ce babu wanda ya kaiwa Hausawa hari hasalima wasu ne suka yi kokarin fashi
  • Odunlami ta kuma ce makirai masu son haddasa fitina ne suka lauya zancen don kawai su dagawa jama'a hankali

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ondo - Rundunar yan sandan jihar Ondo ta bayyana cewa ba a kai kowani harin ramuwar gayya kan al’ummar Hausawa ba a yankin Sabo da ke garin Ondo ko kuma wani yanki na jihar ba, Jaridar The Nation ta rahoto.

Rundunar ta ce harin da aka ce an kai wa al’ummar Hausawa wasu makirai masu son haddasa tashin hankali da fargaba a fadin jihar ne suke shirya zancen.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun harbe mai shayi, direba da 'yan kasuwa a jihar Ondo

Gidan talbijin na AIT ta kuma rahoto cewa kakakin rundunar yan sandan jihar Ondo, Funmilayo odunlami ta karyata rahoton.

Karya ne ba a kashe kowa ba a garin Ondo – Rundunar yan sanda
Karya ne ba a kashe kowa ba a garin Ondo – Rundunar yan sanda Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An dai kawo cewa yan bindiga a yammacin ranar Laraba a yankin sabo da ke garin Ondo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Odunlami ta ce an yi yunkurin yiwa wata mota da ke dauke da albasa da dankali daga Zaria a hanyarta ta zuwa Ore fashi ne.

Ta ce motar ta ya da zango ne a garin Ondo sannan sai wasu yan fashi suka far mata da misalin karfe 01:10.

“A cikin haka ne yan fashin suka harbi direban yayin da karen motar ya tsere da raunin harbi. Harbin ya kuma samu wani mai babur da wani da ke wucewa.
"Sai dai kuma, abun takaici ne cewa wadannan makiran wadanda basu nufin alkhairi basu tabbatar da labarin ba kafin yada wannan karyar domin wadanda fashin ya ritsa da su sun kasance daga kabilar Yarbawa, Igbo da kuma arewa.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC: 'Yan takara na ta bin deliget har otal domin neman hadin kai

“Tuni aka fara bincike kuma ana kokarin ganin an kama maharan.
“Kan haka, kwamishinan yan sandan jihar Ondo, CP Oyeyemi Adesoye Oyediran, ya bukaci mutanen jihar da su kwantar da hankalinsu sannan su yi watsi da wannan labarin karyar, domin makiran na son haifar da rikici mara tushe da tayar da zaune tsaye a jihar.
"Haka kuma ana gargadin masu yada wannan labarin na karya da su daina saboda rundunar ba za ta nade hannunta tana kallo su wargaza zaman lafiyar da ke jihar ba.”

Tsageru sun sace mai daukar hoton gidan gwamnatin jiha, suna neman N50m

A wani labarin, mun ji cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da madaukin hoton gidan gwamnatin jihar Ebonyi, Mista Uchenna Nwube a hanyar Okigwe-Aba-Enugu.

Wannan lamari ya bude jerin tattaunawa tsakanin 'yan jarida da ma'aikatan gidan gwamnati game da lafiyar wanda aka sace, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin nakiya a coci: Ana ta zaben fidda gwani, Tinubu ya tafi jihar Ondo ziyara

Nwube, wanda masu garkuwa da mutane suka ba shi damar kira ta wayarsa, ya shaida wa wasu ‘yan jarida cewa an yi garkuwa da shi ne a ranar Laraba da misalin karfe 7 na dare, Pulse ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng