Wani ‘Dan Majalisa ya shirya zanga-zanga shi kadai a titi a kan harin jirgin Abuja-Kaduna
- Bamidele Salam ya hadu da ‘yanuwan matafiyan da aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja-Kaduna
- Hon. Salam shi ne ‘dan majalisar tarayya mai wakiltar Ede ta Arewa/Ede ta Kudu/Egbedore da kuma Ejigbo
- ‘Dan majalisar ya ce gwamnati ba ta damu da halin da wadannan mutane da aka yi garkuwa da su ke ciki ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - ‘Dan majalisa mai wakiltar Ede ta Arewa /Ede ta Kudu/Egbedore/Ejigbo a majalisar wakilan tarayya, Bamidele Salam, ya fito ya yi zanga-zanga.
Honarabul Bamidele Salam ya yi wannan zanga-zanga ne a dalilin mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su kwanaki a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
Punch ta ce Bamidele Salam yana zargin gwamnatin tarayya da yin sakaci wajen ceto wadannan Bayin Allah da aka yi ram da su tun a karshen watan Maris.
A cewar Salam, ya kamata gwamnatin tarayya ta nemi afuwa wajen ‘yanuwan wadanda aka dauke.
Kamar yadda Legit.ng Hausa ta samu labari, ‘dan majalisar tarayyar ya yi zanga-zangar ne shi kadai a titi a yankin Maitama a babban birnin tarayya Abuja.
Salam ya rike takarda yana mai zaburar da shugaban kasa yi abin da yadace. ‘Dan siyasar na Osun ya yi zanga-zangar ne ba tare da takalma a kafafunsu ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Salam ya zauna da 'yanuwan matafiyan
Rahoton ya ce Hon. Salam ya hadu da ‘yanuwan wadanda abin ya shafa a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuni 2022, domin ganin ya yi bakin kokarinsa a ceto su.
A cewar Bamidele Salam, ‘yanuwan wadannan mutane sun yi abin da za su iya daga bangarensu, don haka ya ce zai yi zama da shugabannin majalisa kan batun.
A nemi afuwarsu - Hon. Bamidele Salam
“Ina tunanin abin farko da ya kamata shugabannin majalisa su yi a kasar nan shi ne a nemi afuwarsu. A ba su hakuri na rashin tausayin da aka nuna.”
“Sun rubuta takarda zuwa ga majalisa, zan yi mamaki idan wannan takarda ta je ga shugaban majalisa, na san ba zai yi wasa da irin ta ba.”
“Jami’an tsaro da majalisar tarayya duk ba su kula su, ko su tuntube su bayan aukuwar abin ba. Su ne ke neman a zauna, kuma hakan bai kamata ba.”
“Ina so in bada hakuri a madadin shugabannin majalisa, kuma in tabbatar masu da cewa za a ji labari mai dadi bayan na saurari labarin nan na su.”
'Yan bindiga su na fada da juna
A farkon makon nan ne aka samu labari cewa mummunar rigima ta kaure tsakanin dakarun Bello Turji da na wani ‘dan bindiga wanda ake kira Dullu.
An kashe Dullu tare da wasu yaransa da suka fitina mutanen garuruwan Shinkafi da Moriki. Yaran wannan 'dan bindiga ne suka fara tsokano su Turji.
Asali: Legit.ng