Rigima ta kaure tsakanin ‘Yan bindiga, su na ta kashe junansu da kansu a jejin Zamfara

Rigima ta kaure tsakanin ‘Yan bindiga, su na ta kashe junansu da kansu a jejin Zamfara

  • Mummunar rigima ta kaure tsakanin dakarun Bello Turji da na wani ‘dan bindiga, Dullu
  • An kashe Dullu tare da wasu yaransa da suka fitina mutanen garuruwan Shinkafi da Moriki
  • Rikicin ya fara ne a sakamakon kashe mutanen Turji a titin Shinkafi-Kaura-Namoda

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Rahotanni daban-dabam sun tabbatar da cewa rigima ta kaure tsakanin miyagun ‘yan bindigan da suka hana Bayin Allah sakat a jihar Zamfara.

Kamar yadda Daily Trust ta fitar a wani rahoto, ana ta rigima ne tsakaninsu Bello Turji yaran Maniya wanda aka fi sani da Dullu a kusa da yankin Shinkafi.

Wannan rikici ya yi sanadiyyar mutuwar Dullu da wasu daga cikin yaransa da kuma wasu ‘yan bindigan da ke tare da gawurtaccen hatsabibin nan, Bello Turji.

Abin ya faru ne a lokacin da yaran Maniya suke hanyarsu zuwa dajin Sububu. Wadannan miyagu sun saba tare Bayin Allah tsakanin garin Shinkafi da Moriki.

Kara karanta wannan

Bayan kwana 40, 'dan Najeriya da ya tuko babu daga London ya iso Legas, hotunansa sun bayyana

Rahoton Daily Trust ya tabbatar da cewa Dullu da Dan Maigari sun hallaka tare da wasu mutum 15.

An tsokano Turji

Kisan wani daga cikin yaran Turji wanda ake kira Na-Sanda ya yi sanadiyyar rigimar. A dalilin haka Turji ya dauki yaransa suka kai wa yaran Maniya hari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan bindiga
Gungun 'Yan bindiga Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An fara kashe yaran Turji ne a kan hanyar Shinkafi-Kaura-Namoda yayin da suke kokarin zuwa asibiti a Kano. Hakan ta sa dakarun Turji suka dauki fansa.

Dan Mai Gari da aka kashe ‘danuwa ne wajen Bashari Maniya – wanda shi ma shahararren ‘dan bindiga ne wanda ya yi kaurin suna a yankin jejin Sububu.

Wata majiya ta ce Turji ya dauke wasu ‘yan bindigan, daga baya ya kashe su. Rahoton ya ce a wajen aka yi watsi da gawar Dullu da sauran wadanda aka kashe.

Kara karanta wannan

Ka taimaka kada ta tayar damu daga gidajenmu: Mazauna garuruwan dake kan titin Abuja-Kaduna

Daily Post ta ce shi kan shi Turji ya rasa yaransa a harin, wasunsu kuma sun samu rauni daga harsashi. Wadanda ake tunanin sun mutu sun kai mutane 44.

Asali: Legit.ng

Online view pixel