Uwa da 'yayanta sun kashe maigida mai rowa saboda cin gadonsa

Uwa da 'yayanta sun kashe maigida mai rowa saboda cin gadonsa

  • Wata mata a jihar Adamawa ta hada baki da 'yayanta wajen kashe mahaifinsu saboda yana da rowa
  • 'Yayansa sun dauki hayar wani makashi ya tayasu kashe mahaifinsu don suyi saurin mallakar dukiyarsa
  • Asirinsu ya tonu kuma Alklali ya bada umurnin jefasu gidan yari yayinda zasu cigaba da gurfana a kotu

Adamawa - Wata matar aure mai suna, Hafsat Saidu, tare da 'yayanta biyu sun kashe mijinta mai suna Saidu Mamman, dan shekara 60 don mallakar dukiyarsa.

'Yayan mutumin, Fai'za da Faisal Saidu, sun biya wani mutumi mai suna Matthew Peter wanda akafi sani da Goga don kashe mahaifinsu saboda yana da tsananin rowa.

Leadership ta ruwaito cewa sun bayyanawa jami'an tsaro cewa N120,000 suka biya Goga don aikata wannan aika-aika.

An garkamesu a a gidan yarin Yola bayan Alkalin kotun Majistare ya bada umurnin jefasu.

Kara karanta wannan

An kuma: Mummunan fashewa ta auku a Kano an rasa shaguna, mutum 20 sun jikkata

Sun kashe mahaifinsu ne ranar 4 ga Afrilu, 2022 a gidansa dake Sanger FUTY a karamar hukumar Girei ta jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Uwa da 'yayanta sun kashe maigida mai rowa saboda cin gadonsa
Uwa da 'yayanta sun kashe maigida mai rowa saboda cin gadonsa Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

An tsinci gawarsa misalin karfe 6 na safe cikin jini kuma aka garzaya da shi asibitin Specialist dake Yola inda aka tabbatar da mutuwarsa.

A cewar Lauyan yan sanda, Sifeto Hamza Abdullahi, hukumar ta samu labarin ne misalin karfe 6:30 na safe a ranar kuma aka damke wadanda ake zargi.

Yace:

"An damkesu kuma sun bayyana cewa lallai hada baki sukayi kuma suka dauki hayar Matthew Peter (ana nemansa har yanzu) suka biyashi N120,000 don ya kashe Saidu."

Lauyan ya bukaci a dage zaman saboda wannan babban laifi ne don yan sanda su samu damar kammala bincike.

Alkalin ya dage zaman zuwa ranar 4 ga Yuli, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel