Neman Kafa Shari'a: CAN Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kama Wasu Malaman Addinin Musulunci a Taraba

Neman Kafa Shari'a: CAN Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kama Wasu Malaman Addinin Musulunci a Taraba

  • Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, reshen Jihar Taraba ta yi kira ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dauki mataki kan wasu malaman addinin musulunci a Taraba
  • CAN ta nuna damuwarta ne bisa wani faifan bidiyo da ya bazu bayan kammala zaben fidda gwani na APC a Taraba inda malaman ke neman a kafa shari'ar musulunci a jihar
  • Kungiyar ta CAN ta nuna rashin gamsuwarta da kiraye-kirayen da malaman suka yi tana mai cewa lamarin zai iya janyo rikicin addini a jihar don haka a dauki mataki a kansu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, reshen Jihar Taraba ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da abin ya shafa su kama tare da bincikar wasu malamai da ke neman a kafa shari'ar musulunci a jihar, rahoton TVC.

Kara karanta wannan

Gumi ya bukaci FG ta kafa ma'aikatar harkokin makiyaya don jin kokensu

Bidiyon da aka danganta shi da wasu malaman addinin musulunci da ke neman gwamnati ta kafa shari'a a jihar ya fito ne jim kadan bayan an sanar da wanda ya lashe zaben fidda gwani na APC.

Neman Kafa Shari'a: CAN Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kama Wasu Malaman Addinin Musulunci a Taraba
Shari'a: CAN Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kama Wasu Malaman Addinin Musulunci a Taraba. Hoto: The Nation.
Asali: UGC

Duk da cewa dai mambobin jam'iyyar ta APC da dama sun ta yin maganganu game da zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan Jihar Taraban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da wadanda ba su gamsu ba sun shigar da korafinsu ga shugbannin jam'iyya, wanda ya lashe zaben tuni ya nemi hadin kai daga wadanda suka sha kaye, amma siyasar da sauya salo bayan malamai sun fara musayar kalamai.

CAN ta nuna rashin gamsuwarta ga malaman addinin musulunci da ke neman ganin a kafa shari'a a Taraba

Shugabannin Tekan Ecwa na CAN, a shafinsu sun nuna damuwa game da bidiyon da ke kira ga cewa a kafa shari'a a jihar bayan Kirista ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Deliget din PDP ya sadaukar da dukkan kudin da ya samu ga al'ummarsa, ya biya wa yara kudin makaranta

Shugbannin Kirista, yayin taron manema labarai a Jalingo sun ce ba su gamsu da bidiyon ba, suna mai kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro su dauki mataki cikin gaggawa don kiyaye afkuwar rikicin addini a jihar, Sahara Reporters ta rahoto.

Kungiyar ta CAN na Jihar Taraba ta bukaci mazauna jihar su cigaba da zama lafiya da juna ba tare da la'akari da banbancin addini ba.

'Batanci: Ba Za Mu Lamunci Kashe Kiristoci a Bauchi Ba Da Sunan Zagin Annabi, CAN Ta Ja Kunnen Musulmi

A wani rahoton, Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta nuna bacin ranta dangane da zargin wata da batanci da aka yi a Jihar Bauchi, inda ta ja kunne akan cewa ba za ta lamunci kisa da sunan batanci ba, Leadership ta ruwaito.

Kungiyar ta CAN kalubalanci gwamnati da kuma jami’an tsaro akan su yi gaggawar daukar matakin da ya dace akan tozarta kundin tsarin mulkin da ake yi kafin gagarumin tashin hankali ya barke wanda za a kasa dakatar da shi.

A wata takarda wacce shugaban kungiyar na reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab ya saki, ya ce CAN ta kula da yada ake amfani da sunan batanci a arewacin Najeriya ana halaka wadanda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ba su karasa halakawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164