Fasto: A coci aka tara buhunnan kudi domin biyan 'yan bindigan da suka sace ni

Fasto: A coci aka tara buhunnan kudi domin biyan 'yan bindigan da suka sace ni

  • Babban limamin coci ya bayyana yadda coci ya tara makudan miliyoyi aka bai wa 'yan bindiga da sunan kudin fansa
  • Malamin ya bayyana cewa, coci ne suka tara kudade a cikin buhu kana suka kai wa 'yan bindigan da suka sace shi
  • Idan baku manta ba, rahotanni sun karade kasar nan da ke nuna cewa, an sace malamin cocin a ranar Lahadi

Legas - Shugaban Cocin Methodist, Samuel Uche, a ranar Talata ya ce an biya Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa kafin 'yan bindiga su sake shi, Channels Tv ruwaito.

A wani taron manema labarai a Legas, malamin ya ce an shirya kudaden ne a buhu biyar na Naira miliyan 20 kowanne, kuma Cocin Methodist a Najeriya ne ya tara kudaden.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi, NNPP da wasu abubuwa 5 da Kwankwaso ya yi magana a hirar da aka yi da shi

Ya kuma yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ko ta jiha, ko sojoji ko ‘yan sanda ba su shiga tsakani ba a lamarin.

Malamin coci ya bayyana yadda aka biya kudin fansa
Garkuwa da mutane: Yadda fitaccen fansa ya ba da fansar N100m ga 'yan bindigan da suka sace shi | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An sace malamin coci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi garkuwa da malamin ne a ranar Lahadi a jihar Abia amma a ranar Litinin aka sake shi.

An yi garkuwa da shugaban cocin ne tare da wasu mutum biyu, Bishop na cocin Methodist da ke Owerri da kuma na'ibinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi dauke su ne da misalin karfe biyu na rana a kan hanyarsu ta zuwa wani shirin coci a Okigwe ta jihar Imo zuwa Isuochi a karamar hukumar Umu Nneochi a jihar Abia.

Satar mutane don neman kudin fansa ya zama ruwan dare a wasu sassan Najeriya, ciki har da yankin Kudu maso Gabas inda aka fi dora laifin ta'addanci kan kungiyar IPOB, mai neman ballewa daga Najeriya.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, IPOB Ta Bayyana Abin Da Ta Sani Game Da Kisar Gillar Da Aka Yi Wa Harira Da 'Yayanta 4 a Anambra

A halin da ake ciki dai, gwamnatin tarayya ta dau mataki mai tsauri kan batun biyan kudin fansa. Kwanan nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan wata doka da ta haramta biyan kudin fansa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Nakiya ta sake tashi a gidan giya yayinda yan PDP ke murnar nasarar Atiku

A wani labarin, kuma dai, an kai harin Bam karamar hukumar Kabba dake jihar Kogi, kwanaki 18 kacal da kai harin farko.

Leadership ta ruwaito cewa wannan karon ana zargin nakiya ce ta tashi a wani gidan giya dake Okepadi, yayinda mambobin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ke murnar nasarar Alhaji Atiku Abubakar a zaben fidda gwanin dan takaran shugaban kasa.

Wannan annobar ta auku ne ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel