Yaro dan shekara bakwai ya mutu cikin rijiya a Kano

Yaro dan shekara bakwai ya mutu cikin rijiya a Kano

Hukumar kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce wani yaro dan shekara bakwai, Umar Ado ya mutu a cikin rijiya a Unguwa Uku by Yarabawa Street a karamar hukumar Tarauni na jihar.

Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saidu Mohammed a ranar Laraban wannan makon kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mohammed ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da yamma a lokacin da marigayin ya tafi rijiyar domin ya diba ruwa.

Yaro dan shakara bakwai ya mutu cikin rijiya a Kano
Yaro dan shakara bakwai ya mutu cikin rijiya a Kano. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Garba Shehu: An sayar da man fetur N600 kowanne lita a mulkin PDP

"Wani Abdulrauf Abba ne ya kira mu misalin karfe 6 na yamma ya sanar da mu. Mun aike da jami'an mu nan take zuwa wurin da abin ya faru suka isa misalin karfe 6.07 na yamma.

"An ciro gawarsa daga rijiyar aka tafi da shi asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano inda aka tabbatar da cewa ya mutu," in ji shi.

A wani rahoton daban, kun ji cewa wata mata ta zame ta faɗa cikin dam a lokacin da ta ke ɗaukan hotuna yayin wata liyafar cin abinci na masoya da aka yi a Chepkiit Waterfalls da ke yankin Nandi.

Ruwa ya yi awon gaba da Dorcas Jepkemoi Chumba mai shekaru 31 a ranar Lahadi yayin da saurayinta Banjamin Kazungu ke amfani da wayan ta yana ɗaukan ta hoto.

Iyalan Miss Chumba da suka fito daga kauyen Kapchorwa a Keiyo ta Kudu sun tare a Chepkiit Waterfalls tun ranar Lahadi da nufin za a gano gawarta.

Masunta a yankin da ke neman gawar ta ba suyi nasara ba a lokacin da ake haɗa wannan rahoton kamar yadda da Nation ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Mun gaji da jan kafa da ka ke yi, ka canja shugabannin tsaro: Hadakar kungiyoyin arewa ga Buhari

Ɗan uwan ta Victor Kiptoo ya roki gwamnatin Uasin Gishu da Nandi su taimake su wurin gano gawar ta.

"Abin ya faru kuma mun rungumi ƙaddara, roƙo kawai muke yi a taimake mu a gano gawar ta," in ji shi.

Shugaban ƴan sanda na yankin Nandi, Samson Ole Kina ya ce ambaliyar ruwa ce ke kawo cikas wurin gano gawar.

Ya bukaci iyalan wacce ta rasun su ƙara haƙuri yayin da jami'an da ke aikin za su cigaba da nazarin lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: