Karin bayani: Kotu ta ba EFCC umarnin ci gaba da garkame tsohon gwamna Okorocha

Karin bayani: Kotu ta ba EFCC umarnin ci gaba da garkame tsohon gwamna Okorocha

  • A yau ne aka gurfanar da tsohon gwamnan jihar Ribas kuma sanata, Rochas Okorocha a gaban wata babban kotun tarayya a Abuja
  • Ana zargin Okorocha ne da karkatar da kudaden kasa lokacin da ya hada kai da wasu kamfanoni a kasar nan
  • Kotu ta ce EFCC ta ci gaba da garkame sanatan har sai an duba batun belinsa kamar yadda rahotanni suka bayyana

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon gwamnan Imo Sanata Rochas Okorocha a hannun hukumar EFCC har sai an yanke shawara kan belinsa.

Okorocha da ke a hannun EFCC, jigo ne a jam’iyyar APC, amini kana abokin harkallar tsohon gwamna, Anyim Nyerere Chinenye, rahoton The Nation.

Za a ci gaba da Rochas Okorocha a magarkamar EFCC
Da dumi-dumi: Kotu ta ba EFCC umarnin ci gaba da garkame tsohon gwamna Okorocha | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Mai shari’a Inyang Ekwo ya ba da umarnin ne a ranar Litinin bayan da Okorocha, Chinenye da kamfanoni biyar suka gurfana a gaban kuliya bisa zarge zarge 17 na halasta kudaden haram da EFCC ta shigar.

Kara karanta wannan

Zamfara: EFCC ta fadi dalilan da suka ja ta kama tsohon gwamnan Arewa

Mai shari’a Ekwo ya dage ci gaba da sauraren karar Okorocha da Chinenye har zuwa ranar Talata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamfanoni biyar din sune: Naphtali International Limited, Perfect Finish Multi Projects Limited, Consolid Projects Consulting Limited, Pramif International Limited da Legend World Concepts Limited.

Ta yaya batun ya faro?

Gurfanar da Okorocha dai na zuwa ne kwanaki uku bayan da ya rasa beli, har sai an yanke hukuncin karar da ya shigar a kan gwamnatin tarayya.

Ya dai bayyana bukatar belinsa ne da cewa shi dan takarar shugaban kasa ne, yana mai jaddada cewa burinsa na siyasa zai shiga cikin hadari matukar ba a ba shi belin ba.

Sai dai mai shari’a Ekwo, a wani takaitaccen hukunci da ya yanke kan neman belin Okorocha a ranar Juma’a, ya ce bai da matsala da ba da belin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta gurfanar da Rochas Okorocha kan zargin damfarar N2.9bn

A maimakon haka, alkalin ya umarci Okorocha da ya sa gwamnatin tarayya ta zo ta kare tsare shi, inji rahoton Channels Tv.

EFCC ta gano sabbin N90bn da AGF Ahmed Idris ya wawure, ya tona asirin minista da wasu jiga-jigan gwamnati

A wani labarin, bincike kan makuden kudaden da hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, game da dakataccen akanta janar na tarayya, Ahmed Idris, ya haura ya kai N170 biliyan, rahoton jaridar The Nation ya bayyana.

Idris, wanda a daren jiya ya ke neman a bada belinsa, ya bayyana sunayen wasu manyan jami'an gwamnati da ke da hannu cikin handamar kudaden kasar da ake tuhumarsa a kai.

Hukumar EFCC ta tuhumi wani babban sakataren gwamnati kan wasu daga cikin kudaden da ake zarginsa da rub da ciki a kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel