Sokoto: An Tilasta Wa Ɗan Majalisa Rabon Kayan Tallafi Da Ya Ɓoye a Gidansa Bayan Wani Ya Kai Wa ICPC Tsegumi

Sokoto: An Tilasta Wa Ɗan Majalisa Rabon Kayan Tallafi Da Ya Ɓoye a Gidansa Bayan Wani Ya Kai Wa ICPC Tsegumi

  • Bala Kokani, dan majalisa mai wakiltar mazabar Kebbe da Tambuwal ya rarraba babura da kekunan dinkin da ya boye a gidansa da ke Sokoto bayan Hukumar Yaki da Rashawa ta ICPC ta tilasta shi
  • Wani ne ya kai korafi ga hukumar ICPC din, inda ya sanar da ita cewa ya ki raba kayan sana’ar ga mutanen mazabarsa wadanda gwamnati ta tanadar don rage rashin ayyukan yi
  • Bayan hukumar ta bincika, maimakon ta tozarta dan majalisar a bainar jama’a, ta tilasta shi rarraba kayan aikin ko kuma ya fuskanci hukuncin abinda ya aikata wanda hakan ya sa ya raba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sokoto - Bayan Hukumar Yaki da Rashawa Mai Zaman Kanta, ICPC ta shiga lamarin, dan majalisa mai wakiltar mazabar Kebbe da Tambuwal, Bala Kokani ya rarraba babura da kekunan dinkin da ya boye a gidansa da ke Sokoto, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaɓen Fidda Gwanin APC: Da Ƙyar Na Sha, Dole Na Tsere Don Kada a Kashe Ni, In Ji Ɗan Majalisa

Hakan ya biyo bayan yadda wani mai fallasa ya kai karar dan majalisar ga ICPC, inda ya sanar da hukumar yadda ya ki rarraba kayan sana’ar wanda hakan na cikin ayyukan da ya dace ya yi wa mazabar.

Sokoto: An Tilasta Wa Ɗan Majalisa Rabon Kayan Tallafi Da Ya Ɓoye a Gidansa Bayan Wani Ya Kai Wa ICPC Tsegumi
Dan Majalisa a Sokoto ya yi rabon kayan tallafi babu shiri bayan ICPC ta gano inda ya boye kayayyakin. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

Kayan, kamar yadda mai korafin ya ce, an tanade su ne don bunkasa tattalin arziki ga mutanen mazabar, wadanda ya kamata ya raba wa jama’a don yaki da rashin aikin yi da kuma bunkasa sana’o’in masa kananun jari tare da koyon sana’a ga marasa su.

Ya so adana kayan ne don siyan kuri’u lokacin zaben 2023

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, mai korafi ya ce, dan majalisar ya yi amfani da damar ne wurin dankare kayan aikin a gidansa da ke jihar don ya rarraba kayan lokacin zaben 2023, don siyan kuri’un jama’a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Ya Isa Haka: Sarkin Musulmi Ya Yi Zazzafan Martani Kan Kisar Harira Da Yaranta 4 Da 'Yan Ta'adda Suka Yi a Anambra

Hakan ya sa hukumar ICPC ta zabura ta fara aiki, ta bibiyi gidan dan majalisa inda ta gano duk kayan da mai karar ya sanar da ita.

Bayan ya samun labarin hukumar ta gano halin da ake ciki, Kokani, dan majalisa karkashin jam’iyyar APC ya nemi kariya daga shugabancin majalisar don gudun a tozarta shi.

ICPC ta amince da cewa ba za ta tozarta dan majalisar ba a gaban jama’a, amma ta tilasta shi rarraba kayan ga mutane cikin gaggawa ko kuma ta hukunta shi.

A ranar 20 ga watan Mayun 2022, Daily Nigerian ta samu takardar da Kokani ya amince da bin sharuddan da hukumar ta kafa masa.

Ya sanar da hukumar rana da lokacin da zai raba kayan

Kamar yadda takarda ta zo:

“Na rubuto wannan takardar ne don in sanar da hukumar cewa zan rarraba kayan ga mutanen yankina a ranar Talata, 24 ga watan Mayun 2022 da misalin karfe 12 na rana a garin Kebbe, hedkwatar karamar hukumar Kebbe da ke jihar Sokoto.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an EFCC sun tasa keyar sanata Okorocha daga gidansa

Da farko dan majalisar don gudun gwamnatin tarayya ta shiga, ya siya duk kayan rabon inda ya killace su har sai zaben 2023 don ya siya kuri’un mutane.

Ana zarginsa ne bayan ganin yadda ake ta zaben fidda gwanin babbar jam’iyyar ana siyan kuri’u daga hannun wakilan jam’iyya ta hanyar ba su kudade da tsadaddun abubuwa.

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

A wani rahoton, Naja’atu Mohammed, mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar ‘Yan sanda, PSC, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda a ranar Alhamis, majalisar jiha, wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Muka Yi Dirar Mikiya a Gidan Okorocha, EFCC Ta Magantu

An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164