Anambra: Osinbajo ya yi martani kan kisan 'yar Arewa da 'ya'yanta 4 a jihar Kudu

Anambra: Osinbajo ya yi martani kan kisan 'yar Arewa da 'ya'yanta 4 a jihar Kudu

  • Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya yi Allah wadai da kashe mata mai ciki da 'ya'yanta a jihar Anambra
  • Ya bayyana haka ne tare da yin bayanai masu dumi game da lamarin, inda yace dole a dauki matakin da ya dace
  • Osinbajo ya koka da cewa, irin wannan mummunan aiki ka ikya kai wa ga tayar da fada tsakanin kabilu a kasar nan

Najeriya - Jaridar Punch ta rahoto cewa, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi martani mai zafi kan yadda wasu 'yan IPOB suka yiwa wata mata 'yar Arewa kisan gilla tare da 'ya'yanta a jihar Anambra.

Osinbajo ya bayyana cewa, wannan mummunan aiki aboin Allah wadai ne, rashin hankali ne, kuma lallai zai iya haifar da rikicin kabilanci a kasar, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rayuwar dan Adam ta yi arha a Najeriya: CAN ta yi Alla-wadai da kisan Fatima da yaranta a Anambra

Osinbajo ya yi Allah Wadai da kashe mata da 'ya'yanta a jijar Anambra
Anambra: Osinbajo ya yi martani kan kisan 'yar Arewa da 'ya'yanta 4 a jihar Kudu | Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

A cewarsa:

“Abin da ya faru a Anambra na kashe wata mata da ‘ya’yanta ya girgiza mu duka. Irin wannan ta'asa ne kuma rashin tausayi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kuma ina ganin ya kamata mu yi taka-tsan-tsan a matsayinmu na al’umma da irin wannan kashe-kashe da ake tafkawa, musamman ma inda a fili ya ke haifar da irin wannan firgici, bacin rai da haifar da wani yanayi da za mu fara samun rigingimun kabilanci da ma duk wata matsalar.
“Kuma ina ganin tilas ne mu yi taka-tsan-tsan tare da yin Allah wadai da shi cikin kakkausar murya, babu wani uzuri ga komai. Kada mu kyale yanayin da za mu kai ga za mu fuskanci mutanen da za su iya yin irin wannan abu.
“Ta yaya za a kashe mace da ‘ya’yanta? Ina ganin wannan mummunan bala'i ne da kowa ya kamata ya la'anta. Shugaban kasa ya yi magana game da hakan kuma ina so in kara fadi da muryata tare da sauran wadanda suka fusata kan lamarin gaba daya."

Kara karanta wannan

Kisan gillan da IPOB suka yiwa Bahaushiya da 'ya'yanta 4: Gwamnan Anambra ya ce ba Hausawa aka nufi farmaka ba

Idan baku manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fusata da mummunan lamarin, ya ya fitar da wata sanarwa ta musamman a kai.

Kashe-kashe a Kudu maso Gabas: Ku tsammaci martani mai tsauri daga gareni, Buhari ga 'yan IPOB

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan rashin imani da ake yiwa bayin Allah da basu ji ba basu gani ba a yankin kudu maso gabas da sauran yankunan kasar.

Shugaban kasar, a cikin wata sanarwa daga kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya gargadi masu aikata ta’asar da su tsammaci mataki mai tsauri daga rundunonin tsaro, Daily Trust ta rahoto.

Fadar shugaban kasar ta kuma yi gargadi kan daukar kowanne irin mataki na ramuwar gayya daga kowane bangare na kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.