Kuma dai: ‘Yan bindiga sun farmaki ofishin yan sanda a Anambra, sun kona motoci

Kuma dai: ‘Yan bindiga sun farmaki ofishin yan sanda a Anambra, sun kona motoci

  • Tsagerun ‘Yan bindiga a Anambra sun kashe mutane hudu a wani farmaki da suka kai wurare daba-daban a jihar
  • Hakazalika, 'yan bindigar sun kona ofishin yan sanda da motocinsu a yankin Anaku da ke karamar hukumar Ayamelum ta jihar
  • Zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin yan sandan jihar ba kan lamarin domin kakakin rundunar ya yi gum da bakinsa

Anambra - Bayan kashe mutane bakwai da suka yi a jiya Lahadi, 22 ga watan Mayu, tsagerun 'yan bindiga sun sake kashe wasu mutum hudu a wurare biyu a jihar Anambra.

Maharan sun kuma farmaki wani ofishin yan sanda a garin Anaku da ke karamar hukumar Ayamelum sannan suka kona motocin da ke wajen, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamna ya saka tukwicin naira miliyan 10 kan makasan dan majalisa a jaharsa

Kuma dai: ‘Yan bindiga sun cinnawa ofishin yan sanda da motoci wuta a Anambra
Kuma dai: ‘Yan bindiga sun cinnawa ofishin yan sanda da motoci wuta a Anambra Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An tattaro cewa kashe-kashen da aka yi, ya wakana ne a garin Ogbunike da ke karamar hukumar Oyi.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa 'yan bindigar sun farmaki kasuwar shanu da ke yankin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An kuma kashe wani mutum daya a garin Peter Obi na Agulu a karamar hukumar Anaocha, inda aka kuma kona wata motar sintiri.

Kakakin yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu, ya ki cewa komai kan lamarin, amma wata majiya ta yan sanda ta tabbatar da faruwar harin na Anaku.

Gwamna ya saka tukwicin naira miliyan 10 kan makasan dan majalisa a jaharsa

A wani labari na daban, gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo ya saka tukwicin naira miliyan 10 ga duk mutum ko kungiyar da za ta bayar da bayanai masu amfani da zai kai ga kama makasan dan majalisar dokokin jihar, Hon Okechukwu Okoye.

Kara karanta wannan

Yan kasar Nijar, da wasu yan bakin haure ke aikin Okada a Legas, Kwamishanan yan sanda

Idan za a tuna an yi garkuwa da mamba mai wakiltan mazabar Gwamna Chukwuma Soludo, Hon Okechukwu Okoye, a makon da ya gabata.

Sai dai kuma, an tsinci kansa a ranar Asabar, 21 ga watan Mayu, a Nnobi da ke karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra, ba tare da gangar jikinsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel