AK9Train: Miyagu sun tuntubi kakakin Sheikh Gumi, sun ba FG wa'adin kwana 7 ko su aiwatar da nufinsu

AK9Train: Miyagu sun tuntubi kakakin Sheikh Gumi, sun ba FG wa'adin kwana 7 ko su aiwatar da nufinsu

  • 'Yan ta'addan da suka sace fasinjoji sama da 60 na jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun tattauna da kakakin Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ta waya
  • Sun sanar da cewa sun bai wa gwamnatin tarayya wa'adin kwana 7 su cika sharuddansu ko kuma su halaka dukkan fasinjojin da suka sace
  • Sun bukaci a sako 'ya'yansu takwas da gwamnati ta kwashe a Kaduna tare da kai su gidan marayu a jihar Nasarawa

Miyagun da suka sace sama da fasinjoji 60 a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, 2022 suna barazanar halaka dukkan wadanda ke hannunsu matukar gwamnatin tarayya ba ta cika sharuddansu ba, HumAngle ta rahoto.

Wannan na kunshe ne a wani sautin sakon murya wanda jaridar Desert Herald ta samu inda 'yan ta'addan suka yi magana da Tukur Mamu, mai magana da yawun Sheikh Mahmud Gumi, fitaccen malamin addinin Islama na garin Kaduna.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun yanka manoma 45 a wani sabon harin Borno

AK9Train: Miyagu sun tuntubi kakakin Sheikh Gumi, sun ba FG wa'adin kwana 7 ko su aiwatar da nufinsu
AK9Train: Miyagu sun tuntubi kakakin Sheikh Gumi, sun ba FG wa'adin kwana 7 ko su aiwatar da nufinsu. Hoto daga HumAnglemedia.com
Asali: UGC

A tattaunawar, mai magana da yawun 'yan ta'addan ya ce lokacin da gwamnatin tarayya ta same su, sun bayyana cewa suna bukatar a saki 'ya'yansu, wadanda su takwas ne kuma daga nan sai su bayyana wadanda za su saki.

Mahaifin yaran wanda ya ke kusa da mai magana da yawun 'yan ta'addan, ya jero sunayen 'ya'yan kamar haka: Abdulrahman, Bilkisu, Usman da Ibrahim wadanda yayi ikirarin an kama su a Kaduna kuma an kai su gidan marayu a Nasarawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da wakilin 'yan ta'addan ya ce yaran takwas ne, sunayen hudu kadai suka laissafo. Sai dai rahoton Desert Herlad ya kara da bayyana sunan wata Juwairiyyah a cikinsu.

Rahoton ya kara da bayyana cewa "Ba mu bukatar kudi. Muna da nagartattun dalilai na yin abinda muka yi. Har sai an cika sharuddanmu, babu wanda za mu saki da ransa ko da hakan na nufin duka su halaka ne. Muna kula da su sosai kamar yadda ku ke gani a hotunan da muka tura muku ta WhatsApp amma muna tabbatar muku ba za mu cigaba ba."

Kara karanta wannan

Ziyara gidan Sarkin Kano: Buhari ya gana da iyalan wadanda bam ya tashi dasu a Kano

'Yan ta'addan sun yi ikirarin cewa, an dage dawo da karakainar jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna da aka sa ranar 24 ga watan Mayu ne saboda su.

Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, NRC ta dage shirin da take na dawo da karkainar jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna bayan wasu lauyoyi sun maka su a kotu a ranar 20 ga watan Mayu kan cewa a dakatar da su har sai sun samar da tsaro daga 'yan ta'addan.

Dage ranar dawowar aikin jiragen kasa yana da alaka da zanga-zanga da 'yan uwan fasinjojin da aka sace suka fito na cewa a fara sako 'yan uwansu kafin a dawo da ayyukan jiragen kasan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel