Ciyar Da 'Yan Makaranta: Gwamnati Za Ta Kashe N999m Kullum Don Ciyar Da Ɗalibai N10m

Ciyar Da 'Yan Makaranta: Gwamnati Za Ta Kashe N999m Kullum Don Ciyar Da Ɗalibai N10m

  • Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za ta rika kashe Naira miliyan 999 a kullum domin ciyar da dalibai miliyan 10 a makarantun frimare a kasar
  • Hakan na cikin tsarin ciyar da yan makaranta na gwamnati ne bayan Shugaba Buhari ya amince a kara kudin da ake kashewa duk dalibi a kullum daga N70 zuwa N100
  • Jagorar shirin, Hajiya Aishatu Digil ne ta bayyana hakan a yau Talata a Abuja wurin taron masu ruwa da tsaki kan yadda za a aiwatar da sabon tsarin

FCT Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za ta kashe Naira miliyan 999 a kowacce rana karkashin shirinta na ciyar da yan makarantun frimare don ciyar da kimanin dalibai miliyan 10 a kasar.

Jagorar shirin, Hajiya Aishatu Digil ce ta sanar da hakan a ranar Talata a Abuja, wurin taron masu ruwa da tsaki kan hanyoyin da za a bi don aiwatar da shi, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Mai hali: An tasa keyarsa magarkama bisa tafka sata a ofishin 'yan sandan Abuja

Ciyar Da 'Yan Makaranta: Gwamnati Za Ta Kashe N999m Kullum Don Ciyar Da Ɗalibai N10m
Ciyar Da 'Yan Makaranta: FG Za Ta Kashe N999m Kullum Don Ciyar Da Ɗalibai N10m. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta, Ministan Jinkai da Walwalar Al'umma, Hajiya Sadiya Farouk ta samu amincewar kashe N100 kan ciyar da kowanne dalibi/daliba a makaranta a kullum, rahoton Vanguard.

Ta ce za a fara ciyar da yan aji daya zuwa uku na frimare su kimanin 9,990,862 da abincin N100 a kullum, kudin zai kama N999,086,200.

"A baya, muna kashe N70 don ciyar da kowanne dalibi a rana tun shekarar 2016, amma shugaban kasa ya amince a kara kudin zuwa N100.
"Muna tare da masu ruwa da tsaki kaman Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Kididdiga ta Kasa da Hukumar Wayar da Kan Jama'a ta Kasa, NOA, da Ma'aikatar Noma da ta Ilimi don tattauna hanyoyin kasafta kudaden.
"Mun zo nan domin duba hanyar da za a fi samun amfani a shirin bisa sabuwar karin kudin da aka samu domin inganta yanayin abincin da aka bawa yara, in ji ta.

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

Ta cigaba da cewa

"Ga yadda za a kashe Naira 100; N70 shine kudin abincin baki daya amma banda kwai, N14 shine kudin kwai da za a aiwatar da hannun hadin gwiwa da Kungiyar Masu Kiwon Kaji na Najeriya.
"Muna shirin samar da 'Larabar Kwai' inda kowanne dalibai za a rika bashi kwai guda daya ranar Laraba.
"N10 kudin masu dafa abinci ne, N11 kuma kudin sinadaran girki sai N1 kuma ta masu kula da ingancin abincin, amma ba dole ba ne."

Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin N64,684 bisa basukan da ƙasar ta ci a ƙasashen waje

A wani labarin, kun ji cewa bisa yawan ‘yan Najeriya da kuma yawan basukan da ake bin ta, kowa ya na da N64,684 a kan sa.

Kamar yadda kowa ya san yawan bashin da Najeriya take ta amsowa daga kasashen ketare, yanzu ko wanne dan Najeriya ya na da bashin $157 ko kuma N64,684 a kan sa.

Kara karanta wannan

Zagin Annabi: Dole A Yi Adalci Kan Kisar Deborah Yakubu, In Ji Amina Mohammed

Bisa wannan kiyasin, masanin tattalin arzikin kasa, Dr. Tayo Bello ya bayyana damuwar sa akai inda ya ce duk da zuzurutun basukan, babu wasu abubuwan ci gaba da aka samar wadanda za su taimaka wurin biyan basukan kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164