Mai hali: An tasa keyarsa magarkama bisa tafka sata a ofishin 'yan sandan Abuja

Mai hali: An tasa keyarsa magarkama bisa tafka sata a ofishin 'yan sandan Abuja

  • A ranar Litinin, 23 ga watan Mayu wata kotun birnin tarayya ta yankewa wani direba hukuncin daurin watanni shida a gidan yari
  • Kotu ta yankewa direban hukuncin ne bisa laifin satar kudi daga hannun abokin zamansa a magarkamar 'yan sanda da ke Abuja
  • A cewar rundunar ‘yan sanda, tun da farko an kama direban mazaunin Abuja ne da laifin satar kayan motsa jiki da batirin mota da kuma waya iPhone

Abuja - Wata kotun unguwar Dei-Dei da ke Abuja, a ranar Litinin, ta yanke wa wani direba mai suna Habib Dada mai shekaru 34 hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, bisa samunsa da laifin satar N13,250 mallakin wani da ake zargi da ke tsare a hannun ‘yan sanda.

Dada da ke Guzape, a kauyen Asokoro, Abuja, ya amsa laifinsa na tserewa daga hannun jami'ai da kuma aikata sata tare da rokon a yi masa sassauci, rahoton Daily trust.

Kara karanta wannan

An ki cin biri, an ci dila: Yadda sabon AGF ke da jikakkiyar tuhumar rashawa da EFCC

Yadda aka daure wani saboda tafka sata a ofishin 'yan sanda
Mai hali: An tasa keyarsa magarkama bisa tafka sata a ofishin 'yan sandan Abuja | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sai dai alkalin kotun, mai shari'a Sulyman Ola, ya bai wa wanda ake tuhuma zabin biyan tarar N40,000 a kan tuhume-tuhumen biyu, sannan ya gargade shi da ya daina aikata laifin.

Mai shari'a Ola ya kuma umarci wanda aka yankewa hukuncin da ya biya N13,200 da ya sata a ofishin ‘yan sanda, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Chinedu Ogada, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin yana tsare ne a magarkamar ‘yan sanda na Efab Estate ranar 29 ga watan Afrilu, bisa laifin satar kayan motsa jiki, waya iPhone da kuma batirin mota.

Ogada ya ce dan sanda ya fito da mutane biyu da masu laifi, daga nan ne wanda ake zargin ya yi amfani da damarsa wajen fauce kudin tare da tserewa daga magarkamar 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Siyasa: 'Yan daba sun farmaki 'yan jarida a taron kamfen din wani gwamnan APC

Mai gabatar da kara ya ce daga baya ‘yan sanda sun gano shi tare da sake damko shi.

A halin da ake ciki, kotun, a wata shari’ar ta daban, ta kuma yanke masa hukuncin daurin wata tara a gidan yari saboda satar kayan motsa jiki mallakin wani uban gidansa.

Ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi da laifin cin amana da sata sannan ya roki kotu da ta yi masa sassauci.

Alkalin kotun, Sulyman Ola, ya baiwa Dada zabin biyan tarar N25,000 tare da umartarshi da ya biya N520,000 a matsayin diyya ga wanda ya yiwa asara.

Rashawar N80bn: EFCC ta sauya wa Akanta-Janar wurin zama daga Kano inda aka kama shi

A wani labarin, hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ta sauya wa babban Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris wurin zama; daga Kano zuwa Abuja.

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

Wasu majiyoyi a hukumar sun shaidawa jaridar The Nation a ranar Talata, 17 ga watan Mayu, cewa an gayyaci ‘yan uwan Idris da ta ta hanyarsu ya aiwatar da zambar da ake tsare da shi akai domin yi masa tambayoyi sosai.

Daya daga cikin majiyar ta shaida wa jaridar cewa: “Hukumar ta dauke AG-F daga Kano zuwa Abuja domin yi masa tambayoyi. Tuni ya fara ba jami'an binciken mu hadin kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.