Sabon nadi: Buhari ya nada gwamna Sule a matsayin mamban majalisar tattalin arzikin zamani
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabbin nade-nade, ya nada gwamna mai ci a wata majalisar fadarsa
- Gwamna Sule na jihar Nasarawa na daga cikin nadin, Buhari ya nada shi mamban kwamitin tattalin arzikin zamani
- Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Nasarawa ta saki, aka kuma mika wa manema labarai
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Nasarawa - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a matsayin mamba a majalisar shugaban kasa kan tattalin arzikin zamani da gwamnatin zamani.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai ga gwamnan, Ibrahim Adra ya fitar kuma ya bayyanawa manema labarai ranar Talata a Lafiya.
The Nation ta ruwaito cewa, sanarwar nadin na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami.
Babban sakataren yada labaran ya bayyana cewa wasikar ta nuna cewa majalisar na daga cikin kokarin aiwatar da manufar tattalin arzikin zamani ta kasa (NDEPS) da kuma tsarin gwamnatin Najeriya a zamanance (NEGMP).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kara da cewa, ministan ya bayyana jihar Nasarawa a matsayin mai matukar muhimmanci ga nasarar ajandar tattalin arzikin Najeriya na zamani, Independent ta tattaro.
Shugaban kasa ne zai rantsar da Gwamna Abdullahi Sule da sauran ‘yan majalisar a wata rana da za a sanar nan gaba.
Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo
A wani labarin, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.
Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.
Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.
Asali: Legit.ng