Dankwali ya ja hula: Bidiyon wata amarya yayin da take yiwa angonta budar kai ya janyo cece-kuce

Dankwali ya ja hula: Bidiyon wata amarya yayin da take yiwa angonta budar kai ya janyo cece-kuce

  • Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar wani bidiyo na shagalin bikin wasu ma'aurata a shafukan soshiyal midiya
  • Sabanin yadda aka saba gani bisa al'ada, dankwali ne ya ja hula a bidiyon domin amarya ce ta yiwa ango budar kai
  • Angon dai ya kasance dauke da lullubi a fuskarsa inda amaryar ta yi masa likin kudi kafin daga bisani ta bude masa fuska

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kamar yadda yake bisa al’adar mallam Bahaushe, a kan yi budar kai a yayin shagalin bikin aure, inda ango zai bude fuskar amaryarsa bayan ya baiwa kawayen amarya tukwici.

Sai dai lamarin ya sauya salo a wani bikin aure da aka yi kwanan nan, inda dankwali ya ja hula.

Dankwali ya ja hula: Bidiyon wata amarya yayin da take yiwa angonta budar kai ya janyo cece-kuce
Dankwali ya ja hula: Bidiyon wata amarya yayin da take yiwa angonta budar kai ya janyo cece-kuce Hoto: northern_hibiscuss
Asali: Instagram

Amarya ta yiwa ango budar kai

A wani bidiyo da ya yi fice a shafukan soshiyal midiya, an gano yadda aka yi budar kan ango sabanin na amarya.

Kara karanta wannan

Amma dai tela bai kyauta ba: Dinkin rigar wani yaro ya girgiza intanet, ana ta cece-kuce

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Angon ya kasance a zaune kan kujera kansa dauke da lullubi yayin da amarya ke tsaye tana yi masa liki, bayan da ta gama sai ta daga mayafin da ya yi lullubi da shi don bayyana fuskarsa.

Nan take sai wajen ya dauki shewa yayin da mutanen wajen ke guda cike da farin ciki.

Kalli bidiyon a kasa:

Mabiya shafukan soshiyal midiya sun yi martani

likakantee ta yi martani:

"Wata sabuwar bidiar kuma tab! Kullun abubuwa gaba sukeyi Allah ya kyauta amin."

elaraab_ ya ce:

"Tasa masa dubu 12,500...ana ta kudii wayake ta budan kai."

ahabas_luxury_store ta yi martani:

"Ni abun da ya banı mamakı me yasa ango zaı saka mayafin mata dama shadda suka saka 2 yards ya lullube da ita."

hajos_collection ta ce:

"Naga abun ne wani banbarakwai wai namiji da suna hajara."

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda matashi ya angwance da amaryarsa baturiya a wani kayataccen biki bayan ta biyo shi Najeriya

luciousbites.ng ta ce:

"Ikon Allah inata jira inga santaleliyA."

Bidiyon yadda matashi ya angwance da amaryarsa baturiya a wani kayataccen biki bayan ta biyo shi Najeriya

A wani labarin, wani matashi mai suna Anuoluwapo, wanda ya tarbi masoyiyarsa baturiya a Najeriya sun shiga daga ciki a wani kayataccen biki da aka yi.

Wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na TikTok ya nuno su tare a cikin wata mota yayin da ya yi masa take da:

“Barkanmu da shiga rayuwar ma’aurata.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel