Ka zabi Ganduje matsayin mataimakin shugaban kasa, an yi kira ga Tinubu

Ka zabi Ganduje matsayin mataimakin shugaban kasa, an yi kira ga Tinubu

  • Jirgin yakin neman zaben Asiwaju Bola Ahmed ya yada zango jihar Kano don haduwa da deleget
  • Mutanen da suka tarbi Tinubu a tashar jirgin saman sun yi kira ga Tinubu ya zabi Ganduje matsayin abokin tafiya
  • Za'a gudanar da zaben fidda gwanin ranar 29 ga Mayu, a farfajiyar Eagle Square dake Abuja

Kano - Daruruwan masoya dan takaran kujerar shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, sun bukaceshi ya zabi Gwamna Abdullahi Ganduje matsayin mataimakinsa inda ya lashe zaben fidda gwani.

Masoyan da suka yiwa tashar jirgin Mallam Aminu Kano zobe don tarbar jigon siyasan, Tinubu, suna yi ihun "Najeriya sai Bola Tinubu tare da Ganduje matsayin mataimakin shugaban kasa."

Tinubu jagora ne a jam'iyyar All Progressives Congress, kuma tsohon gwamnan jihar Legas.

Tinubu ya kai ziyara jihar Kano ne domin ganawa da deleget din jam'iyyar don neman goyon bayansu a zaben fidda gwanin dan takaran shugaban kasa, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Tinubu ya dira jihar Yobe domin janyo hankalin wakilan jam'iyya

Za'a gudanar da zaben fidda gwanin ranar 29 ga Mayu, a farfajiyar Eagle Square dake Abuja.

Masoyan suka ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ka bari Ganduje ya zama mataimakinsa ya kai shugaban kasa mai jiran gado, saboda za kuyi daidai da juna saboda zaku ceto Najeriya daga halin da take ciki."

Ganduje
Ka zabi Ganduje matsayin mataimakin shugaban kasa, an yi kira ga Tinubu Hoto
Asali: Facebook

Wakilan APC da PDP na ta jan miliyoyin kudi yayin da yan takara ke zawarcin kuri’unsu

Yan takara 38 ne ke cikin tseren mallakar tikiti shugaban kasa a manyan jam’iyyun biyu. Yayinda APC ke da 23, PDP na da yan takara 15 da ke neman tikitin shugaban kasar ta.

Wakilan 7,800 a fadin kasar sune za su yanke makomar yan takarar APC 23 a tsakanin 30 ga watan Mayu da 1 ga watan Yuni.

A bangaren yan takarar PDP 15, wakilai 3,700 ne za su yi zabe don daukar mutum daya a tsakaninsu a matsayin wanda zai rike tutar jam’iyyar tsakanin 28 da 29 ga Mayu.

Kara karanta wannan

Tambuwal da Gwamnoni 9 masu neman mulki su na kashe miliyoyi duk rana a hayar jirgi

Kafin ainahin ranar, masu takarar shugaban kasar na ta zawarcin wakilan a jihohin su, suna gwangwaje su da kyaututtuka musamnan na kudi, yayin da suke kokarin tallata kansu, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel