Dalibai sun shiga yanayi a wani bidiyo bayan Shugaban makaranta ya tattara kuɗin WAEC ya tsere

Dalibai sun shiga yanayi a wani bidiyo bayan Shugaban makaranta ya tattara kuɗin WAEC ya tsere

  • Wani bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda aka shanya wasu ɗalibai yayin da suka zo zana jarabawar WAEC
  • Makasudin haka shi ne shugaban makaranta ya tattara kuɗin rijistar WAEC daga hannun ɗalibai kuma aka neme shi aka rasa
  • Bidiyon ya yi bayanin cewa lamarin ya faru ne a jihar Edo kuma fusatattun ɗaliban sun rage fushinsu a kan Tagunan harabar makaranta

Edo - Wani shugaban makaranta wanda har yanzun ba'a gano bayanansa ba ya tattara kuɗin jarabawar fita daga Sakandire WAEC daga bisani aka neme shi aka rasa a jihar Edo.

A wani Bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta wanda Legit.ng Hausa ta gani, shugaban makarantar bai yi wa ɗaliban da suka bashi kuɗi rijista ba, ya shanya su a ranar farko ta fara jarabawa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma da hadiminsa a mahaifar gwamnan Arewa

Daliban SS3 sun hau shirin shugaban makaranta a Ogun.
Dalibai sun shiga yanayi a wani bidiyo bayan Shugaban makaranta ya tattara kuɗin WAEC ya tsere Hoto: @gossipmilltv
Asali: Instagram

A cikin Bidiyon an ga ɗaliban da ke ajin ƙarshe a babbar Sakandire wato SS 3, waɗan da ya dace ace suna cikin aji suna jarabawa, sun fusata suna aika-aika a harabar makarantar.

Rahotanni sun bayyana cewa mamallakin makarantar ya sa ta a kasuwa ƙamar yadda mutane suka ga an kafa allon sanarwa a babbar kofar shiga harabar wurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An hangi ɗaliban suna jifan ginin makarantar da abubuwa daban-daban, suna farfasa tagogi kuma suna karya kayayyakin makaranta.

Duba Bidiyon anan.

Mutane sun yi martani a Istagram

@naomikamara92 ya ce:

"Abun ba dadi amma ya ba ni dariya sosai, ba na mamakin duk abin da mutanen mu na Benin suka yi ba domin za su iya mafi haka."

@Hypegad ya ce:

"Ƙannen mu sun rasa goben su dai a nan wurin, wannan abun tsoro ne."

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan majalisa ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023, Ya lale kuɗi ya sayi Fom

@ngfabs ya ce:

"Shin wannan wasa ne? Wane kalan wasa ne wannan?"

@oluwa_soji7 ya ce:

"Ba abun kunyar da bazaka gani ba a kasar nan ta mu Najeriya duk ƙanƙantar shi."

@chigozie_ehim1 ya yi martani da cewa:

"Kamata ya yi a kama shi cikin gaggawa."

A wani labarin kuma Fusatattun Mutane sun yi ajalin wani dan fashi ɗa dubunsa ta cika a jahar Katsina

Mutane sun yi ajalin mutum ɗaya daga cikin tawagar yan fashi da dubunsu ta cika a karamar hukumar Charanchi ta jihar Katsina.

Bayanai sun nuna cewa yan sanda sun kai ɗauki dan kama yan fashin bayan sun kwace motar wani Abdulmumini a gona.

Asali: Legit.ng

Online view pixel