Fusatattun Mutane sun yi ajalin wani da dubunsa ta cika a jahar Katsina

Fusatattun Mutane sun yi ajalin wani da dubunsa ta cika a jahar Katsina

  • Mutane sun yi ajalin mutum ɗaya daga cikin tawagar yan fashi da dubunsu ta cika a karamar hukumar Charanchi ta jihar Katsina
  • Bayanai sun nuna cewa yan sanda sun kai ɗauki dan kama yan fashin bayan sun kwace motar wani Abdulmumini a gona
  • Kakakin yan sanda reshen jihar Katsina ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce yan sanda sun bazama neman sauran

Katsina - Wani da ake zargin ɗan fashi da makami ne ya rasa rayuwarsa a hannun fusatattun jama'an gari ranar Asabar a ƙaramar hukumar Charanci jihar Katsina.

Punch ta rahoto cewa Mamacin tare da wasu yan tawagarsa huɗu sun kwace wa wani bawan Allah ɗan shekara 52, Alhaji Usman Abdulmumini, motarsa da ta kai darajar miliyan N2.6m.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi ajalin mahaifiya da 'ya'yanta hudu, sun haɗa da wasu mutum biyu

Wata majiya ta ce tawagar yan fashin ta rutsa Abdulmumini yayin da ya je duba gonarsa a kusa da yankin ƙaramar hukumar Kankia, amma yan sanda sun samu kiran gaggawa bayan kwace motar.

Taswirar jahar Katsina.
Fusatattun Mutane sun yi ajalin wani da dubunsa ta cika a jahar Katsina Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kakakin yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, yayin tabbatar da lamarin, ya ce da suka ga zuwan dakarun yan sanda, yan fashin sun yi kokarin kwana don guduwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai fustattun matasa da suka gane abinda ke faruwa, suka yi wa mutanen kofar rago, yayin dukan su ne ɗaya daga ciki ya rasa rayuwarsa.

Yadda lamarin ya faru

Kakakin yan sandan ya ce:

"Ranar Asabar da karfe 12 na rana, muka samu rahoton wasu yan fashi da makami sun farmaki Alhaji Abdulmumini yayin da yaje kewaya gona, suka kwace motarsa Honda ta Miliyan N2.6m."
"Nan take DPO na Charanci ya jagoranci tawagar dakaru suka toshoe hanyar Katsina-Kano a gari. na Charanci. Ana haka sai ga motar amma ɗan fashin ya yi kokarin guduwa, ya haɗu da fushin mutane suka lakada masa duka har lahira."

Kara karanta wannan

Matasan Musulmai sun fito neman matar da ta zagi Annabi ruwa a jallo a Bauchi, an harbe mutum 2

"Da aka bincine cikin motar, jami'an yan sanda sun gano karamr Bindiga Fistol cine da Alburushi guda biyar. A halin yanzu jami'ai sun bazama neman ragowar mutanen, waɗan da suka tsere."

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma da hadiminsa a mahaifar gwamnan Arewa

Wasu miyagu sun kashe ɗan sanda yayin da suka sace shugaban ƙaramar hukumar Keffi, Muhamamd Shehu, da direbansa a jihar Nasarawa.

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun buɗe wa motarsa wuta yayin da ya kusa shiga Gudi, mahaifar gwamna Abdullahi Sule.

Asali: Legit.ng

Online view pixel