Tsohon ɗan majalisa ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023, Ya lale kuɗi ya sayi Fom

Tsohon ɗan majalisa ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023, Ya lale kuɗi ya sayi Fom

  • Tsohon ɗan majalisar tarayya, Dakta Usman Bugaje, ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 da ke tafe
  • Tsohon hadimin Atiku Abubakar ɗin ya ce Najeriya ta tsaya cak tana bukatar jajirtattun shugabanni a zaɓe mai zuwa
  • Ya ce ya ayyana sgiga takara karkashin jam'iyyar PRP ne saboda kyakkywan tubalin da aka gina ta a kai

Abuja - Ɗan fafutukar siyasa kuma tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya Dakta Usman Bugaje, a ranar Jumu'a, ya shiga jerin masu hangen shugabancin ƙasar nan.

Bugaje ya ayyana kudirinsa ne a Abuja bayan ya sayi Fom ɗin takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar PRP, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A cewarsa, Najeriya ta tsinci kanta a cikin wani yanayi da ya zarce tunani da suƙa haɗa da zullumi, tsoro da sauran su.

Kara karanta wannan

2023: APC ko PDP duk wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa zan taya shi murna, Hadimar Buhari

Dakta Usman Bugaje.
Tsohon ɗan majalisa ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023, Ya lale kuɗi ya sayi Fom Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Tsohon ɗan majalisar ya ce Najeriya ta daina motsi, sai dai ta tsaya jiya iyau, ɗaya daga cikin ƙasashe masu hatsari a faɗin duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta rahoto Ya ce:

"A saukake zamu ce Najeriya ba ta aiki amma ta yi muni domin ta zama ɗaya daga cikin wurare masu hatsari a duniya. Don haka mun tsinci kan mu a siraɗi mai hatsari."
"Zaɓen 2023 da ke tafe wata dama ce gare mu ta canza halin da muke ciki ta hanyar zaƙulo shugabanni nagari, masu ilimi kuma waɗan da suka dace da jagoranci."
"Gwamnati a ƙarni na 21 wata haɗakar kimiyyar kasuwanci ne, kuma gwamnatin Zamani na farawa tun daga kudiri wanda ke rikiɗewa zuwa manufa, daga nan sai tsari da sa'aido da aiwatarwa, duk suna bukatar ilimi."

Meyasa ya zaɓi shiga takara a PRP?

Kara karanta wannan

Ana shirin tukarar zaben 2023, Tsohon Ministan Buhari ɗan takara ya fice daga jam'iyyar APC

Bugaje, tsohon mashawarci na musamman ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce jam'iyyar PRP ta ginu ne kan tubalin tainakawa talaka daga hali talauci.

A wani labarin kuma hadimar Buhari tace APC ko PDP duk wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa zata taya shi murna

Hadimar shugaban ƙasa Buhari ta fannin Midiya , Lauretta Onochie, ta ce kowaye INEC ta sanar ya ci nasara zata yi masa murna.

Onochie ta bayyana cewa ba ta damu da ɗan wa ne yanki ko jam'iyya bane, burinta a samu mai kishin ƙasa kamarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel