Bidiyon yadda matashi ya angwance da amaryarsa baturiya a wani kayataccen biki bayan ta biyo shi Najeriya
- Wani matashi mai suna Anuoluwapo a cikin wasu jerin bidiyo da ya saki, ya nuna yadda ya angwance da wata baturiya a wani kayataccen biki
- Wani bidiyo da aka fara saki ya nuna yadda ya cika da farin ciki bayan ya tarbi matar a filin jirgin sama yayin da ta iso Najeriya
- Yan Najeriya da dama sun taya ma’auratan murna, musamman ganin yadda yan uwan Anuoluwapo suka karbi matar hannu bibbiyu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kun tuna matashi Anuoluwapo, wanda ya tarbi masoyiyarsa baturiya a Najeriya? Toh sun yi aure a wani kayataccen biki da aka yi.
Wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na TikTok ya nuno su tare a cikin wata mota yayin da ya yi masa take da:
“Barkanmu da shiga rayuwar ma’aurata.”
Yan uwansa sun karbeta hannu bibbiyu
Wani bidiyon ya kuma nuno su dukka biyun sanye da kayan gargajiya yayin da suka isa gaban mahaifiyar Anuoluwapo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda yake a al’adan Yarbawa, wata daga cikin dangin mijin ta zubawa amaryar ruwa a kafa don nuna cewa zamanta a gidan mijinta zai kasance cikin salama kamar yadda ruwa yake sanyaya jiki.
Kalli bidiyon a kasa:
Bidiyon kasa ya nuna lokacin da aka tarbeta da ruwa:
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:
Isa Thablo ya ce:
“Allah ya albarkaci aurenka dan uwa.”
geesilver ya ce:
“Wannan shine ainahin al’adar Yarbawa…abun takaici mun rasa wannan daraja da dadewa.”
Mammie_phate11 ta ce:
“Ina taya ka murna BarryXchange Allah ya albarkaci gidanka.”
rolandda23 ya ce:
“Kai jama’a wannan ta hadu fa.”
sannisaheed1994 ya ce:
"Allah ya albarkaci gidanka har illa-mashaa- Allah dan uwa.”
Yan mata na kwace mana mazajenmu da shigar banza – Matan aure sun yi zanga-zanga
A wani labarin, wasu matan aure a jihar Imo sun yi zanga-zanga a Owerri kan zargin cewa daliban jami’a mata na amfani da ‘shigar nuna tsaraici da manyan mazaunu’ wajen kwace masu mazajensu.
An gano matan auren kimanin su 10 suna tattaki a fadin wajen dakunan dalibai mata, suna gargadin su da su guje ma shigar banza ko kuma su shirya fuskantar hukunci.
Asali: Legit.ng