Kotu Bada Umurnin a Tsare Matashi, Ɗanladi, Da Ya Kashe Abokinsa Saboda Ya Nemi Budurwarsa

Kotu Bada Umurnin a Tsare Matashi, Ɗanladi, Da Ya Kashe Abokinsa Saboda Ya Nemi Budurwarsa

  • Alkalin kotun Majistare da ke zamanta a Akure, Jihar Ondo ya bada umurnin a tsare matashi, Money Danladi, a gidan gyaran hali
  • An gurfanar da Danladi ne a kotun kan zargin halaka abokinsa, Sunday Babaji saboda ya yi ikirarin ya nemi buduwarsa har ya kwanta da ita
  • Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotu yadda Danladi ya daba wa Babaji wuka a kirji yayin da suke fada hakan ya yi sanadin rasuwarsa

Ondo - Wata kotun majistare da ke zamanta a Akure ta bada umurnin tsare wani mutum mai shekara 22, Money Danladi, kan zargin kashe abokinsa da wuka, Sunday Babaji, saboda fadakan budurwa, rahoton Nigerian Tirbune.

Mai gabatar da kara, Sufeta Nelson Akintimehin ya shaida wa kotu cewa Danlami ya aikata laifin ne a ranar 9 ag watan Mayun 2022, misalin karfe 9 na dare a Badokun Camp via Ode-Aye, karamar hukumar Okitipupa a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan kwashe shekaru 20 a Kurkuku sakamakon masa sharri, ya fito ya tarar dan'uwansa ya sayar da gidajensa 6

Kotu Bada Umurnin a Tsare Matashi, Ɗanladi, Da Ya Kashe Abokinsa Saboda Budurwa
Kotu Bada Umurnin a Tsare Matashi Da Ya Kashe Abokinsa Saboda Budurwa. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Twitter

Mai gabatar da kara ya magantu kan yadda aka kashe Babaji

A cewarsa, wanda ake zargin ya daba wa abokinsa mai shekara 25, Sunday Babaji, wuka ya kashe shi saboda rikici da ya shiga tsakaninsu kan wata budurwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Marigayin da wanda aka yi kara sun yi fada ne saboda wanda aka yi kara ya yi ikirarin marigayin yana neman budurwarsa kuma ya yi ta cika bakin cewa ya kwanta da ita.
"A yayin fadar, Danladi ya daba wa Babaji wuka, hakan yasa ya yi ta zubar da jini har sai da ya mutu."

Danladi, lebura a gona, ya gurfana a gaban kotun kan tuhumar kisa amma bai da lauya mai kare shi don haka kotu ba ta saurari kararsa ba.

Wani sashi na cikin tuhumar ta ce:

"Kai, Money Danladi, a ranar 9 ga watan Mayun 2022, karfe 9 na dare a Badokun via Ode-Oye a Jihar Ondo, ka kashe wani Babaji Sunday, dan shekara 25, ta hanyar daba masa wuka a kirji, hakan ya yi sanadin mutuwarsa."

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

Wannan laifin ya saba wa sashi na 319(1) na Criminal Code, Cap 37, Vol.2 ta dokar Jihar Ondo, 2016, rahoton Naija Dailies.

Mai gabatar da karar ya roki kotu ta bada umurnin a tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali kafin samun shawara daga ofishin shari'ar ta gwamnati, DPP.

Alkalin kotun, Musa Al-Yunus ya bada umurnin a tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali na Olokuta, kafin samun shawarar daga DPP kuma ya dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 25 ga watan Agusta.

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hatsarin mota ya rutsa da dan takarar gwamnan APC a Abuja

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel