Bayan kwashe shekaru 20 a Kurkuku sakamakon masa sharri, ya fito ya tarar dan'uwansa ya sayar da gidajensa 6

Bayan kwashe shekaru 20 a Kurkuku sakamakon masa sharri, ya fito ya tarar dan'uwansa ya sayar da gidajensa 6

  • Wani mutumi da aka yankewa hukuncin kisa ya samu fitowa bayan shekaru 20 da ya kwashe a gidan yari
  • Mutumin, Hatibu Hussein Kifunza, wanda aka 'kalawa sharri ya bayyana abinda ya faru har aka jefashi Kurkuku
  • Fitowarsa ke da wuya, sai ya tarar dan'uwansa ya yi gwanjon gidajensa da ya gina guda shida

A ranar 9 ga Disamba, 2017, wani dan kasar Tanzania mai suna Hatibu Hussein Kifunza, ya kubuta daga gidan yari bayan kwashe shekaru 20 kan laifin da bai aikata ba.

Gabanin sharrin da akayi masa, Hussein Attajiri ne kuma ya mallaki gidaje shida da ya sanya haya kuma yana da wata gidar da yake zama.

Labarin yadda aka kamashi, aka kai shi kotu kuma aka yanke masa hukuncin kisa?

A hirarsa da Afrimax, Hussein wanda yanzu ya zama mai nakasa ya bayyana cewa wata rana ana zaune kalau Sojoji suka gayyacesa bisa laifin da daya daga cikin wadanda ya ba gidan haya ya aikata.

Kara karanta wannan

"Ban Sani Ba Sai Daga Baya" Gwamnan Arewa Ya Umarci a Hanzarta Sakin Wanda Ya 'Zage' Shi a Soshiyal Midiya

Hussein yace kai tsaye ya tafi wajen Sojojin sai ya tarar ana zargin mai hayan da laifin fashi da makami da kuma kisan kai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai Sojojin suka damkeshi shima kan zargin cewa ya baiwa barawo hayan gida saboda tare da shi ake harkar satar.

Daga nan aka gurfanar da shi tare da mai hayan da wasu mutum 6 kuma aka yanke musu hukuncin kisa.

Huseei
Bayan kwashe shekaru 20 a Kurkuku sakamakon masa sharri, ya fito ya tarar dan'uwansa ya sayar da gidajensa 6 Hotuna: Afrimax
Asali: UGC

Dalilin da yasa ba'a kashe shi har yanzu

Hussein yace an garkameshi a kurkukun Ukonga dake yankin Dar es Salaam a kasar Tanzania.

Amma a 2005, Hussein yace Shugaban kasar Tanzania, Benjamin Mpaka, ya musu rangwame ya soke hukuncin kisan da akayi musu amma za'a musu daurin rai da rai.

Bayan shekaru 20 a gidan kaso, sai shugaban kasa, John Magufuli, ya sake shi.

Kara karanta wannan

Daraktan Yakin Neman Zaben Peter Obi Zaiyi Zabe A Kurkuki, Sakamakon Umarnin Kotu Na A Tsareshi

Fitowarsa daga gidan yari

Bayan fitowa daga gidan kaso, Hussein ya tarar dan'uwansa ya sayar da dukkan gidajensa shida ba tare da izininsa ba.

Amma saboda tsoron hada wata alaka da jami'an tsaro ko kotu, Hussein ya hakura ya ki kai dan'uwan nasa kotu kuma yanzu yana zama a gidan mahaifiyarsa.

Yanzu yana fama da ciwon yoyon fitsari kuma yana bukatar taimako.

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel