Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta dage dokar ta sanya bayan da rikici ya barke biyo bayan wata zanga-zanga
  • Rahotanni sun bayyana yadda wasu matasa suka kashe wata dalibar kwaleji tare da banka mata wuta a harabar makaranta
  • Wannan lamari ya jawo cece-kuce bayan kame wasu da ake zargin su suka aikata laifin da ke alaka da addini

Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, a ranar Juma'a, ya dage dokar hana fita da aka kafa a birnin Sokoto, sakamakon rikicin da ya biyo bayan kisan Deborah Samuel.

Gwamnan ya kuma haramta duk wani nau'in zanga-zanga da gangami a fadin a jihar har sai baba-ta-gani, Channels Tv ta ruwaito.

Rahotanni a baya sun ce, wasu fusatattu sun lallasa Deborah Samuel, dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, bisa zarginta da dura ashariya ga manzon Allah SAW.

Kara karanta wannan

Rudani: 'Yan bindiga sun sako hakimin kauyen Kano, sun rike farfesan da ya kai kudin fansa

Gwamnati ta cire dokar hana fita, ta haramta zanga-zanga
Kashe wacce ta zagi Annabi: An dage dokar da aka sanya ta takunkumi a jihar Sokoto | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Rundunar ‘yan sanda a jihar ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan amma ba da jimawa ba zanga-zangar neman a sake su ta karade jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dage dokar hanin na zuwa ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Isah Bajini Galadanci ya sanya wa hannu, kwanaki bayan kafa dokar, inji The Guardian.

Wani yankin sanarwar na cewa:

“Gwamnan ya bukaci jama’a da su kasance masu bin doka da oda kuma su kasance masu son zaman lafiya a kowane lokaci yana mai jaddada bukatar zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar.
“Ya sake nanata bukatar zaman lafiya a matsayin ginshikin da ya dace ga duk wani ci gaba mai ma’ana
“Duk da haka, gwamnati ta haramta duk wani nau’i na zanga-zanga a jihar har sai baba-ta-gani.
“Gwamna Aminu Tambuwal ya godewa al’ummar jihar bisa fahimtarsu wajen bin dokar hana fita da aka kakaba.”

Kara karanta wannan

Zagin Annabi: Kungiyoyin CAN da JNI sun gargadi matasa a kan yin kalaman tunzura

Zanga-zanga bayan zagin Annabi: Tambuwal ya sassauta dokar hana fita a Sokoto

A wani labarin, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya sanar da sake duba dokar hana fita ta sa'o'i 24 da aka kafa a jihar tun bayan tashin hankalin da ya biyo bayan zanga-zangar da wasu mazauna jihar suka fara a ranar Asabar.

A cewar wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Isah Galadanci ya fitar a safiyar ranar Litinin, gwamnati ta sake duba dokar hana fita daga sa’o’i 24 zuwa daga magariba zuwa wayewar gari.

Ya ce an yi hakan ne don baiwa mazauna jihar damar gudanar da harkokinsu na rayuwa kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada, Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.