Manjo Hamza Al-Mustapha: Ina gaje Buhari zan tare a dajin Sambisa saboda dalilai

Manjo Hamza Al-Mustapha: Ina gaje Buhari zan tare a dajin Sambisa saboda dalilai

  • Najeriya ta kara samun dan takarar shugaban kasa, ya kuma bayyana munufofinsa masu karfi a zaben 2023
  • Hamza Al-Mustapha ya bayyana maunfofinsa, inda yace abu ne mai sauki a gare shi ya magance matsalar tsaro
  • Ya kuma ce, dama kawai yake jira, da zarar ya zama shugaban kasa zai koma Sambisa domin gano matsalolin Boko Haram da kuma dakile su

Najeriya - Tsohon soja mai jini a jika, kuma tsohon dogarin shugaban mulkin soja marigayi Janar Sani Abacha ya bayyana abu na farko da zai fara yi idan ya zama shugaban kasar Najeriya bayan zaban 2023 da 'yan kasar ke shirin yi nan kusa.

Manjo Hamza Al-Mustapha, ya ci alwashin karar da 'yan ta'addan Boko Haram, inda yace cikin watanni shida zai yi hakan, domin kuwa dajin Sambisa na jihar Borno zai tare bayan gaje kujerar Buhari domin gane wa kansa hanyar da zai bullowa lamarin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hatsarin mota ya rutsa da dan takarar gwamnan APC a Abuja

Manjo Hamza Al-Mustapha: Ina gaje Buhari zan koma dajin Sambisa da zama
Manjo Hamza Al-Mustapha: Ina gaje Buhari zan koma dajin Sambisa da zama | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Al-Mustapha ya bayyana hakan ne bayan bayyana aniyarsa ta zama shugaban kasa a karkashin inuwa jam'iyyar Action Alliance (AA), kamar yadda kafar labarai ta BBC ta tattaro.

A bayanansa, ya ce zai shafe mako guda a dajin na Sambisa domin gano wasu lamurra da suka cancanta ya mayar da hankali a kai domin tabbatar da Najeriya ta yi sallama da matsalar Boko Haram.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sojojin Najeriya sun lalace

Al-Mustapha ya bayyana damuwarsa ga yadda jami'an sojin Najeriya suka zama lalatattu, wadanda basu dauki kishin kasa a matsayin komai ba, inda yace yana da shirin gyara gidan soja, tare da rage wa wasua jami'ai girma idan suka gagara cimma abin da ya daura su a kai.

A cewarsa:

''Ka ga soja, duk sojan Najeriya ni ina ganinsa daidai yake da dan-sanda na da, saboda sun riga sun zama dan-sandan, kuma 'yan-sandan da kuke da su sun gurbata, sun gurbata. Ni akwai abin da in zan yi a wata shida za ka ji tsoron abin da za a yi amma kuma shi ne gaskiya.'

Kara karanta wannan

Magudi akayi min a 2019, ni na lashe zabe: Atiku Abubakar

''Misali ba shegantakar nan ta Boko Haram ba, wallahi ni zan ce a wata shida indai ba ta yi ba, duka manyan nan sai an rage muku girma, kuma za ku tafi gida, kuma za a hukunta ku kudin da aka ba ku sai kun fid da shi, sai an yi musu probe (bincike).
"A wata shida a matsayina na shugaban kasa zan je Sambiza can zan koma can zan yi hutu, zan yi hutun sati wurin in wani abu ya taba ni ma gani ''

Manufar takarar Al-Mustapha

Al-Mustapha ya bayyana manufarsa ta tsayawa takara da cewa, yana son ganin karshen matsalar tsaro a Najeriya, kuma yana da yakinin yin hakan, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Ya kuma ce, ya zabi jam'iyya mai tasowa ne ganin yadda sauran manyan jam'iyyun siyasar kasar nan suka lalata Najeriya.

Ya kuma zargi gwamnatin Buhari da yin sake wajen sanya ido ga lamurran da ke tafiya a fannin tsaron kasar da kuma mutanen da ke kula da bangarori daban-daban.

Kara karanta wannan

APC da PDP sun fi karfin talaka da matasa: Adamu Garba ya sayi fom din takara a YPP

Al-Mustapha ya ce, kawai 'yan Najeriya su bashi dama, zai zama misalin da kowa zai yi mamaki.

Manjo Hamza Al-Mustapha ya yanki tikitin takara kujerar shugaban kasa a 2023

A tun farko kunji cewa, babban dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya shiga jerin masu neman takara kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Al-Mustapha ya ayyana niyyar takararsa karkashin jam'iyyar Action Alliance AA, rahoton Leadership.

Yayin saya Fam dinsa na takara a hedkwatar jam'iyyar AA dake Abuja ranar Alhamis, jami'in soja mai ritaya ya yi alkawarin kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi yankin Arewa maso gabas da Arewa maso yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.