Gwamnatin Zamfara ta kirkiro sabbin masarautu 2, jimillar masarautun jihar 19 a yanzu

Gwamnatin Zamfara ta kirkiro sabbin masarautu 2, jimillar masarautun jihar 19 a yanzu

  • Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya sanar da kara samar da karin masarautu biyu baya ga masarautu 17 dake fadin jihar
  • Da farko, majalisar jiha ce ta fara zartar da dokar kara sabbin masarautun, sannan shugabannin majalisar suka gabatar a ofishinsa don amincewa
  • Amincewar tazo ne bayan duba matsalar rashin tsaro dake addabar jihar na tsawon shekaru, ya ce hakan zai tunbuko matsalar rashin tsaro tun daga tushe

Zamfara - Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya kara sabbin masarautu biyu akan masarautu 17 da jihar ke dasu.

TVC News ta rahoto cewa, gwamnan ya sanar da hakan ne yayin da yasa hannu a kan dokar, inda ya yi kwaskwarima ga kundin dokar majalisar masarautun a gidan gwamnatin a Gusau, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

Gwamnatin Zamfara ta kirkiro sabbin masarautu 2, jimillar masarautun jihar 19 a yanzu
Gwamnatin Zamfara ta kirkiro sabbin masarautu 2, jimillar masarautun jihar 19 a yanzu. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Masarautu biyun da aka samar karkashin sabbin dokokin sune masarautar Yandoton Daji tare da sarkin da ya samar daga masarautar Tsafe, wanda ya hada da Yandoton Daji, Kizara, Keta, Bawa, Danjibga, Kwanga, Ganuwa, Kuchin Kalgo tare da hedkwatar a Birnin Yandoton.

Dokar, wacce da farko majalisar jiha ta sanar, sannan shugabannin majalisar jiha suka gabatar wa gwamnan a ofishinsa don amincewarsa.

Masarauta ta biyu ita ce Bazai, wacce aka damkata ga sabon sarki wacce ta hada da Bazai, Jangeru, Galadi, Katuru, Birnin Yaro, Tungar Kaho da yankin Tubali, da hedkwata a Jangeru.

"Sabon cigaban zai karfafa ingancin shugabancin gargajiya tun daga tushe. A koda yaushe, a shirye gwamantina take da ta biya bukata, buri da muradin mutane, musamman idan suna da ra'ayin cigaba a wannan mulkin," a cewarsa.

Gwamnan ya yi kira ga sabbin masarautun da su yi amfani da ikonsu da damar da suke dashi wajen tabbatar da hadinbkai, kaunar juna da tarbiyyar al'umma.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bindige jigon jam’iyyar PDP a Akwa Ibom

Jihar da ta dauki tsawon lokaci cikin matsanancin tashin hankali, wanda ya yi sanadiyyar raunata wasu, garkuwa da mutane, salwantar dukiyoyi da rayuka a matakai daban-daban na tsawon shekaru.

Halin da jihar ke ciki ne yasa gwamnatin jihar nada sarakuna da shugabannin gargajiya.

An sa ran sabbin masarautun da aka samar zasu taimaka wajen kawo cigaba a harkar tsaro tun daga tushe, gami da bunkasa tsawon kasa baki daya.

Gwamna Bello Matawalle, wanda aka fi sani da Dodon Maradun na da burin zarcewa a madafun iko a karo na biyu, sannan yana sa ran wadannan matakan zasu taimaka wajen bunkasa harkar tsaro a jihar don tabbatar da ainihin cigaba mai zuwa.

An Dakatar Da Shugaban PDP Na Jihar Zamfara Kan Cin Dunduniyar Jam'iyya

A wani labari na daban, kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar PDP ta Jihar Zamfara ta sanar da dakatar da shugabanta na Jihar, Bala Mande, har sai an kammala bincike da ake yi kan zarginsa da sayar da sirrin jam'iyyar ga wasu mutane don biyan wasu bukatun kansa.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga bayan zagin Annabi: Tambuwal ya sassauta dokar hana fita a Sokoto

A cewar sanarwa sakataren watsa labarai na jam'iyyar, Abba Bello, ya fitar, ya ce an dakatar da shugaban jam'iyyar ne kan zargin cin amanar jam'iyya da wasu abubuwan, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel