Yan bindiga sun bindige jigon jam’iyyar PDP a Akwa Ibom

Yan bindiga sun bindige jigon jam’iyyar PDP a Akwa Ibom

  • Jam’iyyar PDP a jihar Akwa Ibom ta yi rashi na wani babban jigonta, Sir Sylvester. J Ntefre, a ranar Lahadi, 15 ga watan Mayu
  • Guggun yan bindiga ne suka kai farmaki gidan marigayin da ke karamar hukumar Oruk Anam na jihar sannan suka yi awon gaba da shi
  • Kakakin yan sandan jihar, Odiko Macdon ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, 16 ga watan Mayu

Akwa Ibom - Yan bindiga sun harbe jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Akwa Ibom, Sylvester Ntefre, har lahira.

An kashe Ntefre mai shekaru 80 a garin Ekparakwa da misalin karfe 8:00 na safiyar ranar Lahadi, 15 ga watan Mayu.

An tattaro cewa yan bindigar sun farmaki gidansa a Ekparakwa, a hanyar Abak-Ikot Abasi cikin wata bakar motar SUV sannan suka yi ya harbi kan mai uwa da wahabi don tsoratar da makwabta kafin suka yi awon gaba da shi, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Yan bindiga sun bindige jigon jam’iyyar PDP a Akwa Ibom
Yan bindiga sun bindige jigon jam’iyyar PDP a Akwa Ibom Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An rahoto cewa karar harbin ne ya janyo hankalin matasa a yankin inda suka hada hannu da yan sanda wajen fatattakar yan bindigar, lamarin da ya tilastawa maharan barin motar da suka zo da ita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani shaida ya sanar da Premium Times cewa an yi musayar wuta tsakanin masu garkuwa da mutanen da yan sandan a yayin fatattakar nasu.

Daga baya aka tsinci gawar Mista Ntefre kusa da wani daji da harbin bindiga.

Kakakin yan sandan jihar Akwa Ibom, Odiko Macdon ya tabbatar da lamarin a ranar Litinin.

Macdon ya ce kwamishinan yan sandan jihar ya bukaci mika lamarin ga mataimakin kwamishina da ke kula da binciken manyan laifuka.

Ya bayar da tabbacin cewa za a kama wadanda suka aikata laifin.

Marigayin ya kasance jigon garin kuma tsohon shugaban rusasshiyar jam’iyyar All Nigeria Peoples Party na jihar.

Kara karanta wannan

Hotunan Malami Mai Koyar Da 'Yahoo-Yahoo' Da Ɗalibansa 16 Da Aka Kama a Gidan N3m

Daga baya ya koma jam’iyyar PDP lokacin mulkin Gwamna Victor Attah inda aka nada shi Shugaban hukumar kula da harkokin karamar hukuma.

Rikici: 'Yan sanda sun kwamushe mutum 4 bisa laifin kisa da kone wani mutum a kan N100

A wani labarin, ‘Yan sanda a jihar Legas sun kama wasu mutane hudu da ake zargin sun yi wa wani David Imoh mai shekaru 38 kisan gilla ta hanyar kone shi a yankin Lekki Phase One na jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, kama mutunen a ranar Lahadi.

A cewar Mista Hundeyin, wanda Sufeto na ‘yan sanda ne, ba a yarda da daukar doka a hannu a jihar Legas ba, ya kuma gargadi jama’a da su guji irin haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel