Yada barna: Gwamnatin Buhari ta gana da Facebook, ta nemi kassara lagon IPOB a kafar

Yada barna: Gwamnatin Buhari ta gana da Facebook, ta nemi kassara lagon IPOB a kafar

  • Alhaji Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu na Najeriya, ya yi wata muhimmiyar ganawa da wata tawagar Facebook
  • A wajen taron, ministan yada labaran ya shaidawa wakilan Facebook cewa su daina barin kungiyar ta IPOB tana amfani da dandalinsu wajen tada zaune tsaye
  • Mohammed ya ce gwamnatin Najeriya za ta sanya ido sosai kan Facebook da sauran kafafen sada zumunta don tabbatar da an samar da wannan bukata

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Alhaji Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu, ya bukaci Facebook da sauran kafafen sada zumunta da su daina barin haramtacciyar kungiyar IPOB tana amfani da dandalinsu wajen tayar da rikici da haifar da kiyayyar kabilanci a Najeriya.

Sanarwar da Segun Adeyemi, mai taimakawa Mohammed kan harkokin yada labarai ya fitar ta nuna cewa ministan ya yi wannan kira ne a Abuja ranar Talata, 17 ga watan Mayu, a wata ganawa da wata tawaga daga Facebook, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta jero sharudan da za su sa a hana mutum takara a 2023 bayan ya saye fam

Lai Mohammed ya gana da Facebook, ya nemi wata babbar bukata
Tsaro: Gwamnatin Buhari ta gana da Facebook, ta nemi kassara lagon IPOB a kafar | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya ce tun da aka haramta kungiyar IPOB tare da bayyana kungiyar a matsayin ta ‘yan ta’adda, Facebook ba ta da hujjar barin tsarinta ga kungiyar don ci gaba da barna na nuna kiyayya da tada zaune tsaye a kasar.

A cewar ministan:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Na kira wannan ganawa ne domin mu tattauna yadda ‘yan aware da ‘yan mulkin kama karya, musamman wadanda ke zaune a wajen kasar nan ke amfani da shafin Facebook wajen haddasa rikici da kyama tsakanin kabilu a Najeriya.
“Kowane dalili ne, da alama yanzu sun zabi Facebook a matsayin dandalin da suke so. Kuma kayan aikinsu sun hada da yada barna, kalamai masu tada hankali da kalaman kiyayya.
"Suna amfani da hanyar watsa shirye-shirye a Facebook don isa ga mabiyansu, wadanda suka kai dubunnai. Suna yiwa wadanda ke adawa da ta'addancinsu lakabi da 'yan zagon kasa' wadanda dole ne a kai musu hari, a kai su mayanka kuma a kashe su.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano

"Suna amfani da Ingilishi da harshensu na gida yadda ya dace da su."

Ayyukan IPOB a Facebook na matukar tasirin gaske - Mohammed

Da yake karin haske, Mohammed ya ce ayyukan haramtacciyar kungiyar suna da tasiri a rayuwa, inji PM News.

A cewarsa:

"Ta hanyar nuna kiyayya da tayar da hankali, ana kashe mutane yayin da ake kai hari da lalata dukiyoyin jama'a da na gwamnati. Hukumomin tsaro da sauran abubuwan gwamnati su ne abin da suke hara.”

Ministan ya ce duk da yawan korafe-korafen da ake yi a Facebook kan ayyukan kungiyar ta IPOB, babu wani abu da kamfanin ya yi na dakile wuce gona da iri da kungiyar ke yi a dandalin na sada zumunta.

Mohammed ya ce nan da kwanaki masu zuwa gwamnati za ta fara sanya ido a kan Facebook da sauran manhajoji domin tabbatar da an bi wannan kira, yayin da take kara kaimi wajen wayar da kai wajen amfani da kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Sokoto: An ayyana neman wadanda aka gani a bidiyon kone dalibar da ta zagi Annabi

An bindige tsagerun IPOB da ke addabar jama'a a jihar Anambra

A wani labarin, an harbe wasu ‘yan bindiga biyu da ke tilasta dokar “zama-a-gida” da haramtacciyar kungiyar IPOB ke kakabawa jama'ar jihar Anambra.

A cewar rundunar ‘yan sanda, an kashe su ne a hanyar Umunze a karamar hukumar Orumba ta Kudu a Anambra ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce jami’an da ke sintiri kan hana aikata laifuka sun yi arangama da tsagerun dake addabar jama'ar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.