Da Dumi-Dumi: An fara harbe-harben bindiga a wurin da 'Tukunyar Gas' ta fashe a Kano

Da Dumi-Dumi: An fara harbe-harben bindiga a wurin da 'Tukunyar Gas' ta fashe a Kano

  • Rahoto daga wurin da tukunyar Gas ta fashe a jihar Kano ya nuna cewa jami'an tsaro sun harba bindiga don tarwatsa mutane
  • Tun farko wasu yan daba ne suke kokarin farmakan sojoji da duwatsu, hakan ya tilasta yin kokarin korar su daga wurin
  • A halin yanzun dai jami'ai na cigaba da kokarin ceto waɗan da abun ya shafa, mutum 9 ne suka rasa rayuwarsu zuwa yanzu

Kano - Ƙarar harbe-harben bindiga ya tashi sosai a a wurin da tukunyar Gas ta fashe a yankin Sabon Gari, jihar Kano ranar Talata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro ne suka saki harbin domin tarwatsa dandazom mutanen da suka mamaye wurin.

Tun da farko dai wasu matasa yan isakan gari ne suka fara yunkurin faramakan sojoji da duwatsu amma a halin yanzun ƙura ta fara lafawa.

Kara karanta wannan

Fashewar tulun iskar gas: Hukuma ta bayyana adadin mutanen da suka mutu a iftila'in Kano

Wurin da abun ya fashe a Kano.
Da Dumi-Dumi: An fara harbe-harben bindiga a wurin da 'Tukunyar Gas' ta fashe a Kano Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

Yayin da wakilin jaridar ke aikin kawo rahotanni kai tsaye daga wurin, ya ce jami'an tsaro sun saki harbi a saman iska domin tsoratarwa da tarwatsa dandazon mutanen wurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu bayanai sun nuna cewa yayin da ake cigaba da aikin ceto a wurin, wasu yan daba sun fara amfani da abinda ya faru suna fasa shagunan mutane da gidaje.

A halin yanzun, Jami'ai na cigaba da aikin kawar da mutanen da lamarin ya shafa a lokacin da muka kawo wannan rahoton an tabbatar da mutuwar mutum huɗu.

Iyaye sun kwashe ƴaƴan su daga makarantu

Hotunan da bidiyoyin da mutane suka yaɗa a kafafen sada zumunta ya sa iyaye tururuwar zuwa ɗakko 'ya'yan su daga makarantu.

Mutane sun rufe shaguna, yayin da wasu rahotanni suka nuna cewa yan daba sun soma amfani da yanayin da mutane ke ciki suna shiga gidaje da shaguna.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Iyaye sun fara tururuwar kwashe 'ya'yan su bayan abu ya Fashe da ɗalibai a Kano

Akwai wasu bidiyoyi da suka nuna ɗalibai na gudu kayan makarantar da ke jikinsu da alamun jini a jiki sun watsu a kafafen sada zumunta.

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya naɗa sabon shugaban masu yi wa ƙasa hidima NYSC

Shugaban ƙasa Buhari ya naɗa Birgediya Janar Mohammed Fada, daga jihar Yobe a matsayin sabon shugaban NYSC ta ƙasa.

Sabon shugaban zai karɓa ne daga hannun DG mai barin gado, Manjo Janar Shu'aibu Ibrahim, wanda wa'adinsa ya ƙare.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel