Wani Uba ya kai ƙarar ɗansa da ya yi kokarin raba shi da rayuwarsa
Ke duniya, ina zaki da mu ne? irin wannan rayuwa na wannan zamani ya zama abin ban tsoro, musamman yadda imani yayi karanci a zuciyoyin mutane, ba musulman ba, ba kirista ba.
A nan ma wani matashi ne mai shekaru 33, mai suna Muhammad Isiyaku, ne ya zabura tare da yunkurin kashe mahaifinsa a unguwar Bolari, cikin gari Gombe, inda har ya yanke shi da wuka, inji rahoton jaridar Rariya.
KU KARANTA: Rikicin Kwankwaso da Ganduje ya ruruta ayyukan yan bangan siyasa a jihar, jama’a sun koka
Majiyar Legit.ng ta ruwaito sakamakon kaduwa da mahaifin ya yi, tare da gudun kada dan nasa ya sake zabura da nufin kashe, sai mahaifin da kansa ya kai karar dan nasa gaban Kotun majistri dake garin Gombe.
Shi kuwa Alkalin Kotun, Alkali Garba AbubakarDule bayan zuzzurfan bincike ya tabbatar da gaskiyar maganan mahaifin yaron, Malam Isiyaku, kuma ba tare da bata lokaci ba ya yanke masa hukuncin da ta dace da shi.
Alkali Garba ya kafa hujja ne da sashi na 168 da sashi na 78 na kundin hukunta manyan laifuka, inda ya yanke ma mai laifin hukuncin watanni 60 a gidan Kurkuku, tare da horo mai tsanani.
A kwanakin baya ma an samu wani matashi da ya hallaka mahaifinsa a jihar Bauchi, saboda mahaifin ya gargade shi akan shan wiwi. Kai, Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng